2027: Ta Yiwu Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Hade da El-Rufai, Hadimin Atiku Ya Magantu
- Yayin da ake ta shirin siyasar 2027, an yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi zai hade da Nasir El-Rufai a jam’iyyar SDP
- Kakakin kamfe na dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar shi ya bayyana haka a yau Juma’a 22 ga watan Maris a shafin X
- Daniel Bwala ya ce Obi zai bar jam’iyyar LP ne yayin da kungiyar NLC ke kokarin kwace ragamar shugabancin jam’iyyar gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Daniel Bwala, Kakakin kamfen dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce akwai yiwuwar ruguntsumin siyasa a kwanakin nan.
Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai su na shirin hadewa saboda zaben 2027.
Wani hasashe aka yi kan Obi, El-Rufai?
Bwala ya ce Obi zai watsar da jam’iyyar LP zuwa SDP saboda rikicin shugabanci da jam’iyyar tasa ke fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran na APC a yau ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ce El-Rufai ya na shirin barin jam’iyyar APC mai mulkin kasar.
“Ana zargin Peter Obi zai hade da Nasir El-Rufai a jam’iyyar SDP yayin da kungiyar NLC ta shirya kwace shugabancin jam’iyyar LP.”
“Ruguntsumin siyasa zai faru a wannan kwanakin amma babu abin da zai hana Shugaba Tinubu barci wanda ya san lungu da sakon siyasa.”
- Daniel Bwala
Jita-jitar ficewar El-Rufai daga APC
Wannan hasashe ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai zai bar jam’iyyar APC.
Hakan ya biyo bayan ziyarar sa tsohon gwamnan ya kai a ofishin jam'iyyar SDP a birnin Abuja.
Jita-jita yayin da Ribadu ya ziyarci El-Rufai
A baya, mun ruwaito muku cewa hadimin Shugaba Tinubu a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu ya ziyarci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ribadu ya kai ziyarar ce yayin da ake yada jita-jitar cewa El-Rufai na shirin watsi da jam’iyyar APC yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Asali: Legit.ng