Ribadu, FFK zuwa Ningi: El-Rufai Ya Ruda APC, Ya Tada Kura Kwatsam a Siyasar Najeriya

Ribadu, FFK zuwa Ningi: El-Rufai Ya Ruda APC, Ya Tada Kura Kwatsam a Siyasar Najeriya

Abuja - Nasir El-Rufai ya dawo gaban shafukan jaridu da gidajen talabijin bayan an rage jin duriyarsa a fagen siyasar Najeriya.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Legit ta fahimci kwanan nan tsohon gwamnan na Kaduna ya dawo daga kasar Masar, daga dawowarsa ya jawo abin magana.

A rahoton nan, Legit ta tattaro jeringiyar ziyarce-ziyarce da Malam Nasir El-Rufai ya kai a ‘yan kwanakin nan da suka motsa kasa.

Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai ya fara jawo surutu da cece-kuce a Najeriya Hoto: @realFFK, @MuyiwaAdekeye
Asali: Twitter

Su wa Nasir El-Rufai ya ziyarta?

1. Ribadu, jagororin APC da Nasir El-Rufai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanaki aka ji Mai ba Shugaban kasa shawara a harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da wasu jagororin APC sun ziyarci Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malam Nasiru El-Rufa'i ya gana da fitaccen sanatan PDP, hotuna sun bayyana

Sauran ‘yan tawagar da suka zauna da tsohon gwamnan na jihar Kaduna sun kunshi irinsu Kashim Ibrahim-Imam a birnin Abuja.

2. Nasir El-Rufai a sakatariyar SDP

A lokacin da ake rade-radin Nasir El-Rufai zai sauya-sheka ne, sai aka gan shi a sakatariyar jam’iyyar adawa ta SDP a birnin Abuja.

Muyiwa Adekeye ya shaidawa duniya cewa mai gidansa ya ziyarci shugaban SDP na kasa, Shehu Gabam ne a matsayinsu na abokai.

3. Abdul Ningi ya zauna da El-Rufai

Kwanaki bayan dakatar da Abdul Ningi daga majalisa saboda zargin cushe a kasafin kudi sai aka gan shi ya hadu da Nasir El-Rufai.

An fara yada jita-jita cewa Sanata Ningi zai hada-kai da Atiku Abubakar a kafa sabuwar jam'iyya, batun da aka karyata tuni.

4. Femi Fani Kayode da El-Rufai

Wata ziyara da ba da mamaki ita ce ta tsohon Ministan na harkar Abuja da tsohon abokinsa a gwamnatin tarayya, Femi Fani Kayode.

Kara karanta wannan

2027: Ta yiwu dan takarar shugaban kasa ya hade da El-Rufai, Hadimin Atiku ya magantu

An ji Femi Fani Kayode yana jinjinawa Malam El-Rufai bayan zaman nasu. FFK yana cikin manyan abokan hamayya kafin dawowa APC.

El-Rufai ya ba yaronsa gudumuwa

Kwanaki kun ji labari Muhammad Bello El-Rufai ya yi bayanin gudumuwar da Malam Nasir El-Rufai ya ba shi da kamfen 2023.

Duniya ta ji yadda aka gamsar da tsohon Gwamnan Kaduna a kan yaransa ya fito takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel