Wata Sabuwa: Ana Zargin Shugaban APC da Wasu Kusoshi Suna Yunƙurin Tsige Gwamnan PDP

Wata Sabuwa: Ana Zargin Shugaban APC da Wasu Kusoshi Suna Yunƙurin Tsige Gwamnan PDP

  • Matasan jihar Ribas sun yi ikirarin cewa shugaban APC, Cif Tony Okocha da wasu jiga-jigai na kulle-ƙullen kifar da Gwamnatin Simi Fubara
  • Gamayyar ƙungiyoyin shugabannin matasan sun jaddada cewa a shirye suke su ruguza duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaɓaɓɓiyar gwamnati
  • Sai dai Mista Okocha ya musanta wannan zargin, yana mai bayyana shi da tsantsar ƙarya da yaudara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gamayyar shugabannin matasan ƙabilun jihar Ribas (RSEYLC) ta caccaki shugaban kwamitin riƙo ƙwarya na jam’iyyar APC a jihar, Cif Tony Okocha.

Shugabannin matasan sun zargi Mista Okocha da wasu manyan ƙusoshin siyasa da cewa suna ƙulla wata maƙarƙashiya domin kifar da gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano

Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas
Shugabannin matasa sun fallasa wani makircin juyin mulkin farar hula a Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a sanarwa da gamayyar ƙungiyoyin ta miƙa wa jaridar Leadership a Fatakwal mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Dakta Legborsi Yamaabana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan Ribas sun aike da sakon gargaɗi

Kungiyar ta sha alwashin cewa mambobinta za su duk mai yiwuwa wajen rusa duk wani yunkurin na kifar da gwamnatin jihar Ribas mai ci.

Wani sashen sanarwan ya ce:

"Gamayyar ƙungiyoyin shugabannin matasan ƙabilu ta samu labarin tuggun da muƙaddashin shugaban APC, Tony Okocha, ke kitsawa tare da wasu ƴan korensa domin juyin mulkin fararen hula a Ribas.
"Suna ƙulla makirci ne da nufin hamɓarar da zababbiyar Gwamnatin Mai girma Sim Fubara.
Mun yi tir da wannan makirci na zagon kasa ga tsarin dimokuradiyya da tada zaune tsaye a jihar.
"Muna gargadin Tony Okocha da masu taya shi cewa duk wani yunkuri na kifar da gwamnatin jihar Ribas zai fuskanci turjiya mai ƙarfi nan take daga shugabannin matasan Ribas."

Kara karanta wannan

Cushen N3.7trn: Shugaban majalisar dattawa zai yi murabus saboda kalaman PDP? An bayyana gaskiya

Shugaban APC a Ribas ya yi martani

Amma da yake martani, shugaban APC na jihar, Cif Tony Okocha, ya kalubalanci Dakta Yamaabana, da ya bayar da kwaƙkwarar shaida domin tabbatar da ikirarinsa na shirin kifar da gwamnatin Fubara.

Jagoran APC na jihar ya ce zargin ba wai karya ne kaɗai ba, yaudare ce tsantsa inda ya yi kira ga jama’a da suyi watsi da shi gaba daya, rahoton Gazette.

Okocha, wanda ya yi magana ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Vincent Gbosi, ya musanta duk wani yunkuri na kifar da gwamnatin farar hula a jihar.

Wike ya fice daga PDP zuwa APC?

A wani rahoton kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙara jaddada cewa har yanzu shi mamban jam'iyyar PDP ne duk da ƙoƙarin wasu jiga-jigai na ganin an kore shi.

Tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana haka ne yayin hira da wasu zaɓaɓɓun yan jarida a Abuja, ya ce babu abin da ya canza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel