Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Aka Shigar da Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Aka Shigar da Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano

  • Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan ƙarar da aka nemi hana Abba Gida-Gida naɗa ciyamomin rikon kwarya a kananan hukumomin Kano
  • Alkalin kotun mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, ya kori ƙarar a zaman ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024
  • Ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bayan samun takardar janyewa daga mai shigar da ƙara, Haruna Abbas Babangida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta kawo ƙarshen karar da aka shigar gabanta kan batun naɗa kwamitocin riko a kananan hukumomi 44 na jihar.

Kotun ta yi fatali da karar wadda ta nemi a hana Gwamna Abba Kabir Yusuf naɗa ciyamomin rikon kwarya da muƙarrabansu da zasu tafiyar da harkokin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Ana cikin azumi 'yan ta'adda sun kai mummunan hari a jihar Arewa

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
An janye ƙarar da aka maka gwamnan Kano kan naɗa kantomomi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Karar ta kuma roƙi kotun ta umarci gwamnatin tarayya ta daina turo kuɗaɗen kananan hukumomi sakamakon karewar wa'adin zaɓaɓɓun ciyamomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda zaman shari'ar ta kaya a Kano

Yayin da aka dawo zaman ci gaba da sauraron ƙarar ranar Alhamis, alƙalin kotun mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, ya kori ƙarar gaba ɗaya, kamar yada Daily Trust ta ruwaito.

Mai shari'a Liman ya bayyana cewa ya samu takardar janye karar daga mai shigar da ƙara, Haruna Abbas Babangida, mazaunin karamar hukumar Shanono.

Sai dai lauyan mai shigar da kara, Abdu Fagge, ya shaida wa kotun cewa ba shi da masaniya kan haka kuma ba shi ya bayar da takardar janyewar ba.

A nasa ɓangaren, lauyan gwamnati, H. H. Suleiman, mataimakin daraktan kula da kararrakin jama’a, ya shaida wa kotun cewa ya samu takardar janyewa daga mai kara.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun shari'ar Musulunci ta raba auren Sunnah kan dalili 1 tak a watan Ramadan

Wane hukunci kotu ta yanke kan ƙarar?

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya ce tun da kotun ta samu sahihiyar takardar janyewar mai ɗauke da sa hannun mai ƙara, ta kori ƙarar gaba ɗaya.

A makon jiya kotun ta umarci ɓangarorin biyu su dakatar da komai da ya danganci naɗa ciyamomin riƙon kwarya har sai an yanke hukuncin karshe.

Amma kwana guda bayan umarnin kotun, gwamnan Kano ya kaddamar da kwamitocin riko na kowace karamar hukuma, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Barista Tukur Badamasi, lauya mai zaman kansa ya yi gajeren fashin baƙi kan shari'rar, inda ya faɗawa Legit Huasa cewa kotu ba ta da wani zaɓi illa ta kori ƙarar gaba ɗaya.

"Zaman shari'a ya kare tunda mai kara ya janye, ya kamata dai a ce ya sanar da lauyansa kuma takardar ta hannun lauyansa ya dace ta biyo, amma abun mamaki ba haka ta faru ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana zargin shugaban APC da wasu ƙusoshi suna yunƙurin tsige gwamnan PDP

"Amma tun da kotu ta gamsu da sahihancin takardar, ba ta da wani zaɓi face ta sallami ƙarar kasancewar ɓangaren wanda ake ƙara ba su yi musu ba."

Kotu ta tsare hadimin gwamnan Osun

A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta fara sauraron karar da aka gurfanar da wanda gwamnan jihar Osun ya naɗa a muƙami kan tuhume-tuhume 10.

Alkalin kotun ya umarci a tsare Mista Olalekan Oyeyemi a gidan yarin Ile-Ife har zuwa zama na gaba wanda za a yanke hukunci kan bukatar beli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel