Sanata Yari Ya Hada Kai da Atiku Domin Kirkirar Sabuwar Jam’iyya a 2027? Gaskiya Ta Fito

Sanata Yari Ya Hada Kai da Atiku Domin Kirkirar Sabuwar Jam’iyya a 2027? Gaskiya Ta Fito

  • Sanata Abdul’aziz ya yi martani kan jita-jitar cewa su na hadaka domin kirkirar sabuwar jam’iyya kan zaben 2027
  • Yari ya yi wannan martanin ne bayan an yada labarin shirin dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar kan zaben 2027
  • Sai dai Yari ya musanta labarin inda ya ce wannan labari ba shi da tushe bare makama wanda ya kamata a yi watsi da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Yayin da ake yada cewa dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar na shirin kirkirar sabuwar jam’iyya, Sanata Abdul’aziz Yari ya yi martani.

Yari ya karyata cewa ya na daga cikin wadanda ke shirin kirkirar sabuwar jam’iyya kan zaben 2027 da ake tunkara.

Kara karanta wannan

Sanata Yari zai hada kai da Atiku domin kafa sabuwar jam’iyya? Gaskiya ta bayyana

Sanata Yari ya yi martani kan jita-jitar cewa su na hadaka da Atiku domin kafa sabuwar jam'iyya
Sanata Yari ya karyata hadaka da Atiku kan zaben 2027. Hoto: Abdul'aziz Yari.
Asali: Facebook

Martanin Sanatan kan jita-jitar

Sanatan ya bayyana cewa har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne zai ci gaba da kasancewa a cikinta inda ya yi fatali da jita-jitar, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan martani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da bangaren yada labarai na sanatan suka sake wanda Legit ta samu.

“Ofishin yada labaran Sanata Abdul’aziz Yari da ke wakilar Zamfara ta Yamma ta karyata rahoton da ake yadawa a kirkirar sabuwar jam’iyya.”
“Sanatan wanda ya na daga cikin shugabannin jam’iyyar APC ya kasance mai biyayya ga jam’iyyar kuma mai son ci gabanta.”
“A matsayinsa na dan Majalisa, Yari ya na aiki kafada da kafada da mambobin Majalisa ta 10 domin dakile matsalolin da suka addabi kasar.”

- Abdul’aziz Yari.

“Yari ya kasance mai biyayya ga jam’iyyar kuma ya himmatu wurin yin aiki da Shugaba Bola Tinubu domin kawo ci gaban Najeriya.”

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

- Abdul’aziz Yari

Martanin Atiku kan labarin da ake yadawa

Wannan martani na Yari na zuwa ne bayan rahoton cewa Atiku ya na hada kai da wasu domin kirkirar wata jam’iyya ciki har da Sanata Abdul Ningi.

Rahoton ya ce Atiku ya yi hakan ne yayin da ke kokarin kwace mulkin Najeriya a hannun APC a zaben shekarar 2027, cewar Naija News.

Har ila yau, Atiku daga bisani ya musanta labarin inda ya ce ya maida hankali ne wurin kawo hadin kai a tsakanin jam’iyyun adawa.

Yari ya raba kayan abinci

Kun ji cewa, Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, Abdul’aziz Yari ya shirya rabon kayan abinci a watan Ramadan.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin wani irin hali na tsadar rayuwa a fadin Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel