Zargin SSS Kan El-Rufai Ya Sa Majalisar Dattawa Ta Ki Tabbatar Da Shi, Sabon Rahoto Ya Bayyana

Zargin SSS Kan El-Rufai Ya Sa Majalisar Dattawa Ta Ki Tabbatar Da Shi, Sabon Rahoto Ya Bayyana

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewa dalilai na tsaro ne suka hana a tabbatar da El-Rufai
  • Sai dai wani sabon rahoto ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ba a tabbatar da El-Rufai cikin ministocin Tinubu ba
  • Rahoton ya nuna cewa zarge-zargen take haƙƙin bil'adama da kuma kalamai masu haɗari da ke gaban DSS kan El-Rufai ya janyo ma sa tsaiko

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai na daga cikin mutane uku da Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatarwa a matsayin ministoci.

Sauran mutanen biyu da majalisar taƙi tabbatarwa su ne Sani Danladi daga jihar Taraba, da kuma Stella Okotete daga jihar Delta.

An bayyana dalilan ƙin tabbatar da El-Rufai
Sabon rahoto ya bayyana cewa binciken DSS ya hana a tabbatar da El-Rufai. Hoto: Godswill Obot Akpabio, Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Dalilin da ya sa majalisa ta ƙi tabbatar da El-Rufai

Wani rahoto na baya-bayan nan da jaridar Premium Times ta wallafa, ya nuna cewa korafe-korafe masu yawa da aka shigar gaban jami'an tsaro na farin kaya (SSS) kan El-Rufai ne suka janyo ma sa cikas.

Kara karanta wannan

"Akwai Lauje Cikin Nadi, Ba Za Mu Yarda Ba", Majalisar Malamai A Kaduna Ta Tura Sako Ga Sanatoci Kan El-Rufai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga ciki ƙorafe-ƙorafen da aka shigar akwai na zargin take hakkin bil'adama da kuma yin kalamai masu haɗari a bainar jama'a.

Ƙin tabbatar da El-Rufai da Majalisar Dattawa ta yi, ya bai wa 'yan Najeriya da dama mamaki, musamman in aka yi la'akari da irin gudummawar da ya bai wa Shugaba Tinubu.

Rahoton na Premium Times ya bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen da aka shigar a kan El-Rufai ba ɓoyayyu ba ne.

Malaman Kaduna sun buƙaci a tabbatar da El-Rufai

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoto kan buƙatar da majalisar malaman jihar Kaduna suka miƙa ga Majalisar Dattawa, na ta yi gaggawar tabbatar da El-Rufai matsayin minista.

Majalisar malaman ta bayyana matakin ƙin tantance El-Rufai a matsayin wani abu na ɗaukar fansa da wasu ke shirin yi.

Ta ce masu ƙoƙarin ganin ba a tabbatar da El-Rufai ba sun tsorata ne tun lokacin da suka ga sunansa cikin waɗanda a naɗa ministoci.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Tsohon Na Hannun Daman Peter Obi Ya Roki Majalisa Ta Tantance El-Rufai

Shehu Sani ya yi wa El-Rufai shaguɓe

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shaguɓen da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi wa Nasir El-Rufai biyo bayan ƙin tabbatar da shi a matsayin minista.

Shehu Sani ya ce cikin waɗanda majalisa ta ƙi tabbatarwa akwai wani mai tsattsauran ra'ayi da bai kamata ya riƙe muƙamin siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel