Yayin da Ake Samun Matsala a Aure Kan Wasu Dalilai a Kano, Majalisa Ta Dauki Mataki Don Dakile Haka

Yayin da Ake Samun Matsala a Aure Kan Wasu Dalilai a Kano, Majalisa Ta Dauki Mataki Don Dakile Haka

  • Yayin da matsalar rashin gwaji kafin aure ke dagula al’amura, Majalisar jihar Kano za ta dauki muhimmin mataki kan haka
  • Majalisar za ta kafa dokar tilasta masu niyyar yin aure kan gwajin cututtukan kanjamau da ciwon hanta da kuma sikila
  • Kudirin wanda ya riga ya wuce karatu a biyu a zaman Majalisar zai tilasta gwajin cututttukan saboda matsalolin da ake samu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Majalisar Dokokin jihar Kano za ta kafa dokar tilasta masu niyyar aure gwajin cututtuka kafin aure.

Kudirin wanda ya riga ya wuce karatu a biyu a zaman Majalisar zai tilasta gwajin cutar kanjamau da ciwon hanta da ciwon sikila.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam ta dakatar da sayar da kayan abinci kan farashi mai rahusa, ta faɗi dalili 1 tak

Majalisar Kano za ta dauki muhimmin mataki kan masu shirin yin aure
Majalisar Kano za ta tilasta gwaji kafin aure a fadin jihar baki daya. Hoto: Kano Assembly, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Wane doka Majalisar Kano ke kokarin yi?

Dan Majalisar mazabar Takai, Musa Ali Kachako shi ya gabatar da kudirin inda ya koka kan yadda ake samun matsalolin bayan aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takai ya ce jihar na fama da matsalolin karuwar cutar kanjamau inda ma’aurata ke yin aure ba tare da gwaji ba, cewar Daily Trust.

Ya ce idan har aka tabbatar da dokar za ta kare rayukan mutane da dama da kuma yaduwar cututtuka masu hatsari.

Sauran jihohi da sun dabbaka dokar

Ha ila yau, Aliyu Sa’ad wanda ke wakiltar mazabar Ungogo ya ce jihohin Jigawa da Katsina da Kaduna sun aiwatar da irin haka don kare lafiyar jama’a.

Aliyu ya ce jihar Kano ganin yadda ta ke da yawan jama’a dole ta dabbaka dokar don kare lafiyar jama’a, The Whistler ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa kwamiti mai bangarori uku na ba shi shawara kan tattalin arziki

Kakakin Majalisar, Isma’il Falgore ya tura bukatar ga kwamitin lafiya a Majalisar inda ake tsammanin dawo da rahoto cikin makwanni hudu.

Abba Kabir ya gargadi jami’an SSO

A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabri ya gargadi jami’an SSO da ke kula da inganta ilimi a jihar kan ayyukansu.

An dauki jami’an ne don tabbatar da kula da harkar ilimi a jihar wanda za su na karbar alawus musamman wadanda aikinsu ya yi kyau.

Gwamnan ya ce duk wanda aka samu matsala a karkashin kulawarsa zai iya fuskantar hukunci ko rashin biyan alawus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel