An Shiga Halin Ha’ula’i Yayin Da ’Yan Ta’adda Suka Hallaka Kakakin APC a Jihar Plateau

An Shiga Halin Ha’ula’i Yayin Da ’Yan Ta’adda Suka Hallaka Kakakin APC a Jihar Plateau

  • An hallaka wani jigon jam’iyyar APC a jihar Plateau yayin da ya kai ziyarar jana’iza a wani yankin jihar
  • An ruwaito cewa, wasu tsageru ne suka ude masa wuta a daidai lokacin da yake a wani otal da ke jihar
  • Ya zuwa yanzu, jam’iyyar APC bata fitar da sanarwa a hukumance ba kan wannan babban rashin da ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Plateau - An nqalto cewa, an harbe Sylvanus Namang, kakakin jam’iyyar APC a jihar Plateau a yankin Pankshin na jihar.

Wannan na fitowa ne daga bakin wani jigon jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa a yayin da yake zantawa da Daily Trust.

Kara karanta wannan

An bankado wani shirin Ganduje na tilasta gwamna mai ci komawa APC don kwace jihar, bayanai sun fito

A cewarsa, kakakin na APC ya mutu sakamakon raunuka da ya samu a wani harin ta’addanci da aka kai masa.

An kashe kakakin APC nAMANG a jihar Plateau
Yadda aka hallaka shugaban APC a Plateau | Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waye mamacin a duniyar siyasa Plateau?

Da yake bayyana kadan daga halayensa, jigon ya ce Namang ya aksance mutumin kirki kuma abin dogaro a jam’iyyar APC a jihar.

Ya kuma bayyana cewa, nan ba da jimawa jam’iyyar za ta sanar da al’umma batun rasuwarsa a hukumance.

Majiya ta tattaro cewa, an harbe Namang ne a wajen wani dakin otal dinsa, yayin da wasu tsageru suka bude wuta da misalin karfe 7:30 na sanyin safiya, rahoton Leadership.

Meye ya kai jigon APC yankin?

Majiyar ta kuma bayyana cewa, mamacin ya bar gida ne a ranar Asabar zuwa taron jana’iza da aka gudanar Pankshin, inda anan ne aka hallaka shi.

Jihar Plateau na daya daga jihohin Arewacin Najeriya da ke yawan fama da rikicin ‘yan ta’addan da ma kashe-kashe babu haira babu dalili.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

An hallaka jigon APC a Kogi

A wani labarin, an shiga tashin hankali a ranar Lahadi yayin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki mazauna yankin Oganienugu a karamar hukumar Dekina da ke jihar Kogi.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun hallaka mutane da dama a wannan mummunan harin.

An tattaro cewa, ‘yan ta’addan sun shiga kauyen ne da tsakar dare, inda suka fara harbin kan uwa da wabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel