Kamfanin Ajaokuta: Majalisa Za Ta Binciki Gwamnatin Yar’adua, Jonathan da Buhari Kan Fitar da $496M

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa Za Ta Binciki Gwamnatin Yar’adua, Jonathan da Buhari Kan Fitar da $496M

  • Majalisar dattawa za ta fara bincike kan yadda aka ɓatar da dala miliyan 496 da aka ce an fitar don farfaɗo da kamfanin karafa na Ajaokuta
  • Majalisar ta yi mamakin yadda har yanzu kamfanin Ajaokuta da na NIOMCO ba sa aiki duk da kashe masu kudi daga 2008 zuwa yau
  • Mr. Barau Jibrin ya kafa kwamiti da zai binciki wannan badakalar bayan da Sanata Natasha ta gabatar da kudirin gaban majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar dattawa ta kafa kwamiti da zai gano dalilin da ya sa har yanzu kamfanin karafa na Ajaokuta da kamfanin hakar ma'adanai (NIOMCO) ba sa aiki.

Wannan binciken zai yi nazari kan zargin dala miliyan 496 da aka fitar tun a gwamnatin marigayi Umaru Yar'Adua a shekarar 2008 har zuwa karshen mulkin Buhari.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun kafa kwamiti ya binciki bashin da Gwamnatin Buhari ta dumbuzo a CBN

Majalisar dattawa za ta binciki badakalar kamfanin Ajaokuta
Majalisar ta yi mamakin yadda kamfanin karafa na Ajaokuta ke ci gaba da tabarbarewa. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban majalisar, Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya sanar da kafa kwamitin, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yar majalisar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ce ta gabatar da kudirin kafa kwamitin, wanda majalisar ta amince.

Jerin sunayen mambobin kwamitin

Daily Post ta ruwaito cewa Sanata Adeniyi Adegbonmire daga Ondo ta tsakiya ne zai jagoranci kwamitin, sai sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Kawu zai zama mataimakin shugaba.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da; Mrs Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi tsakiya), Onawo Mohamed (PDP, Nasarawa ta Kudu), Joel Ewomazino (PDP, Delta ta Kudu) da Onyesoh Heacho (PDP, Rivers ta Gabas).

Sauran su ne; Abdullahi Yahaya (PDP, Kebbi ta Arewa), Patrick Ndubueze (APC, Imo ta Arewa), Tokunbo Abiru (APC, Lagos ta Gabas) da Osita Ngwu (PDP, Enugu ta Yamma).

Mr. Jibrin ya nemi kwamitin ya haɗa rahotonsa nan da makonni biyu tare da miƙa sa ga majalisar don tattaunawa.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta amince da wani muhimmin nadin da shugaba Tinubu ya yi

Abin da kudirin Natasha Akpoti-Uduaghan ya kunsa

Mrs Akpoti-Uduaghan ta ce akwai lamarin cin hanci da rashawa a lalacewar kamfanin karafa na Ajaokuta.

Sanatar ta nemi majalisar ta yi binciken yadda aka ɓatar da dala miliyan 496 da aka ce gwamnatin tarayya ta ba kamfanin GINL don farfaɗo da Ajaokuta da kamfanin NIOMCO.

Biyo bayan karanta kudirin, majalisar ta yanke shawarar gayyatar ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da suke da hannu a fannin karafa.

Mambobin majalisar da suka goyi bayan kudirin

Sanatan Ogun ta Yamma, Olamilekan Adeola ya goyi bayan kudirin, inda ya koka kan yadda ake biyan ma'aikatan kamfanonin albashi da daloli.

Sani Musa, sanatan Neja ta Gabas, shi ma ya yi korafi kan yadda har yanzu kamfanin karafa na Ajaokuta bai fara aiki ba duk da an kashe masa makudan kudade.

Mafi akasarin sanatocin sun amince da wannan kudiri na Akpoti-Uduaghan bayan da mataimakin shugaban majalisar ya nemi a kada kuri'a akan sa.

Kara karanta wannan

Yayin da ake samun matsala a aure kan wasu dalilai a Kano, Majalisa ta dauki mataki don dakile haka

Buhari ya yi shirin farfaɗo da kamfanin Ajaokuta?

Tun a shekarar 2020, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya, karkashin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da shirin farfado da kamfanin karafa na Ajaokuta.

Shugaba Buhari ya nada kwamitin a ranar 11 ga watan Mayun 2020 karkashin jagorancin Boss Mustapha da nufin farfado da kamfanin bayan shekaru 40 yana zaune ba aiki.

Ko a lokacin, sai da gwamnatin Buhari ta nemi taimakon wani kamfani mai suna Afrexim da kuma wani kamfanin kasar Rasha bayan da ta cimma yarjejeniya da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel