Gwamnan Jihar Arewa Ya Sharewa Ma’aikata Hawaye Bayan Kuncin da Aka Saka Su, Ya Fadi Dalilin Hakan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Sharewa Ma’aikata Hawaye Bayan Kuncin da Aka Saka Su, Ya Fadi Dalilin Hakan

  • Gwamnatin jihar Plateau ta sharewa wasu ma’aikata da aka dakatar hawaye bayan ba da umarnin dawo da su bakin aikinsu
  • Akalla ma’aikata dubu 3,879 ne suka samu wannan damar bayan dakatar da su kan binciken hanyar da aka bi wurin daukarsu
  • Wannan mataki na gwamnatin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnan, Samuel Jatau ya fitar a birnin Jos

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya mayar da ma’aikata dubu 3,879 da aka dakatar a jihar.

Ma’aikatan da ake magana akansu su ne wadanda tsohowar gwamnatin Simon Lalong da dauke su aiki.

Gwamnan PDP ya mayar da ma'aikata bakin aikinsu bayan kammala bincike
Gwamna Mutfwang ya dawo da ma'aikata 3,879 bakin aikinsu. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Menene dalilin dakatar da ma'aikatan a Plateau?

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bankado hanyoyi 32 na safarar abinci daga Najeriya zuwa kasashen waje

Mayar da ma’aikatan bakin aikinsu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnan, Samuel Jatau ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce ma’aikatan sun fito daga ma’aikatu da hukumomi 42 a jihar wadanda aka dauke su karkashin kulawar hukumar ma’aikatan jihar.

Wannan mataki ya kawo karshen binciken da ake yi kan takardunsu da kuma hanyar da aka bi wurin daukarsu aiki.

Gwamnati ta dakatar da daukar aiki a watan Yunin 2023 har zuwa lokacin da kwamitin da aka kafa don bincike su bayar da rahoto.

Zargin take hakkin Musulmai a Plateau

Har ila yau, a cikin sanarwar gwamnatin ta bukaci daukar sabbin ma’aikata a makarantun gaba da sakandare bayan soke dibar aikin da suka yi a baya.

Har ila yau, a jihar Plateau da ake zargin ana take hakkin Musulmi, kungiyar MURIC ta yi alkawarin kawo karshen lamarin.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kano da sauran jihohi 3 da aka gudanar da mummunar zanga-zanga a Najeriya

Kungiyar ta ce za ta bi dukkan hanyoyin da suka dace karkashin dokar kasa don kare hakkin nasu da ake zargin takewa a jihar.

Makinde ya kara wa’adin biyan kudin rage radadi

Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya yi umarnin kara wa’adin biyan kudaden rage radadin cire tallafi har watanni shida.

Gwamnan ya ba da umarnin ne yayin da wa’adin da aka bayar a farko zai kare a watan Maris da zamu shiga.

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar suka sake shiga mummunan yanayi a ‘yan kwanakin nan kan tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel