APC da Dan Takararta Sun Rufe Karar da Suke Na Kalubalantar Zaben Gwamnan PDP, Bayanai Sun Fito

APC da Dan Takararta Sun Rufe Karar da Suke Na Kalubalantar Zaben Gwamnan PDP, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake ci gaba da shari’ar zaben jihar Bayelsa, dan takarar APC, Timipre Sylva ya rufe karar da ke kalubalantar zaben da su ke yi
  • Sylva na kalubalantar zaben ne wanda aka gudanar a watan Nuwambar shekarar 2023 da Douye Diri na jam’iyyar PDP ya yi nasara
  • Jam’iyyar APC da Sylva sun rufe karar tasu ne bayan gayyatar masu ba da shaida har mutane 52 don su ba da shaida kan zaben

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa – Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva ya rufe karar da ya ke yi kan jami'yyar PDP.

Sylva da jam’iyyar APC na kalubalantar zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Nuwambar 2023.

Kara karanta wannan

Wata sabuwar zanga-zanga ta barke a sakatariyar jam’iyyar APC kan wani dalili 1 tak

APC ta janye karar zaben gwamnan PDP duk da gabatar da shaidu
Sylva ya janye karar da ya ke yi kan Douye Diri na Bayelsa. Hoto: Douye Diri, Umar Ganduje, Timipre Sylva.
Asali: Facebook

Wane mataki Sylva da APC suka dauka?

Sai dai sun rufe karar tasu ne bayan gayyatar masu ba da shaida har mutane 52 don su ba da shaida kan almundahana da aka yi a zaben, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Timipre ya kasance a wurin ba da shaidar inda wani tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya ba da shaidar irin badakalar da aka gudanar.

Tsohon kwamishinan Akeem Alausa ya gabatar da shaidu masu karfi inda ya musanta cewa ya na yi wa Sylva aiki ne a lokacin zabe.

Ya ce duk da jam’iyyu 16 suka yi takara a zaben bai yi wa kowace shaida ba sai APC kuma a kananan hukumomi guda uku ne kacal, cewar Tribune.

Matakin da alkalin kotun ya dauka

Kananan hukumomin da ya ke da shaidun sun hada da Nembe da Ogbia da kuma karamar hukumar Southern Ijaw.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da shaidun zaben gwamnan Kogi a harabar kotun Abuja

Alkalin kotun, Mai Shari’a, Adekunle Adeleye ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar 4 ga watan Maris.

Alkalin ya dage wannan shari’ar ce saboda bai wa wadanda ake zargi damar kare kansu kan zargin badakala a zaben.

APC ta tafka asara a Kano

Kun ji cewa wasu jiga-jigan APC a Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne ya karbi sabbin tuban inda ya musu alkawarin cewa sun zama daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel