Masoya Sun Fara Zuga Farfesa Isa Ali Pantami Ya Fito Takarar Gwamna a Zaben 2027
- Akwai masu ganin Isa Ali Ibrahim Pantami zai dace da mulkin jihar Gombe, ana ba shi shawarar ya nemi takarar gwamna
- Masu kaunar malamin ‘dan siyasar sun hango shi a gidan gwamnati duk da ba a fara buga gangunan zaben 2027 tukun ba
- A gefe guda, wasu suna shakku game da farin jini da karbuwar da shehin zai yi musamman a kudancin jihar Gombe
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Gombe - Wata ziyara da Isa Ali Ibrahim Pantami ya kai zuwa mahaifarsa, ta jawo surutu a kafofin sada zumunta na zamani.
Kwanan nan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci garin Gombe, hotunan da ya wallafa a X sun tabbatar da farin jininsa.
Sai Isa Ali Ibrahim Pantami a 2027
Ganin yadda Gombawa suke farin ciki da ganin tsohon ministan tarayyar, sai aka fara ba shi shawarar tsayawa takara a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu wannan tunani suna ganin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami zai iya samun mulki bayan wa’adin Inuwa Yahaya ya cika.
Gwamna Inuwa Yahaya zai bar ofis ne a Mayun 2027, tun a shekarar 2019 ya shiga ofis.
Hadimin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Bashir Ahmaad wanda ya taba neman tutar takara a APC ya tada kura a X.
Bashir Ahmaad ya ce
"Gombe, gobe ta Allah ce.”
Sani Waspaping ya yi irin wannan magana a shafinsa, tuni dai aka yi ca a kan matashin.
Umar Naira ya rubuta:
“Kwanan nan zamu fara kira ga malam yayi takaran gwamna in shaa Allahu.”
“Kawai wanda nake tausayi shine wanda ya yarda yayi takara da shi. Allah kara daukaka da yawan masoya.”
Wani kuma ya ce:
“Gwamna Pantami insha Allahu rabbi”
Pantami: "A yi hattara da 'yan siyasa malam"
Wasu mutane kamar Mukhar Abubakar kuwa har su Farfesa Pantami a kujerar gwamna, ya samu tikiti kuma ya lashe zabe.
Al-Mustapha Maska kuwa bai tare da wadannan, yake cewa mutuncin malamin shi ne ya raba kan shi da shiga harkar siyasa.
Idris Ahmad Gale ya ba malamin shawarar cewa ba a Gombe kurum ake zabe ba, akwai sauran kananan hukumomi a jihar.
Ashraf Babagana ya ja-kunnen tsohon ministan, yake nuna masa za a cinye masa kudi da sunan za a tsaida shi takara ne.
Muzammil Adamu kuwa ya ce malam an koma siyasa a karshe, ganin an san shi wajen koyar da addinin musulunci a kasar.
Pantami zai shiga siyasar jam'iyya?
Jibril Aliyu ya ce shehin yana da farin jini, kuma yana sa ran zai kai labari a 2027.
Da alama mutane kamar Abdul Kano, Abdullah HD da Aluta Virus za su goyin bayan takarar Pantami a ko wace jam’iyya ya tsaya.
Kano: Hisbah v Murja Kunya
Ana da labari lauyoyin Murja Ibrahim Kunya sun ce matakin da hukumar da ke kula da asibitoci ta Kano ta dauka kuskure ne.
A.U Haji ya ce dole ‘yan uwa da lauyoyin Murja Kunya su san halin da ta ke ciki idan ba ta da lafiya ne, ba a fara mata allurai ba.
Asali: Legit.ng