Tsohon Gwamna Ya Tona Boyayyun Bayanai a Kan Bashin da Buhari Ya Karbo

Tsohon Gwamna Ya Tona Boyayyun Bayanai a Kan Bashin da Buhari Ya Karbo

  • Ayodele Peter Fayose bai ga dalilin yabawa Muhammadu Buhari ba, ya ce gwamnatinsa ba alheri ba ce ga al’umma
  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti ya zargi tsohon shugaban kasa da cin wasu bashin da sai nan da shekaru 50 za a fara biyansu
  • Idan za a bi ta Fayose, babu dalilin da zai sa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya rika yabawa magabacinsa, Muhammadu Buhari

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Ayodele Fayose ya yi gwamna sau biyu a jihar Ekiti, ya soki yadda Mai girma Muhammadu Buhari ya yi mulkin kasar nan.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Channels, Ayodele Fayose ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da lalata tattali.

Kara karanta wannan

Atiku ya karantar da Tinubu, ya fadawa Shugaban kasa hanyar gyara a saukake

Bola Ahmed Tinubu/Ayodele Fayose/Muhammadu Buhari
Ayo Fayose yana ganin Buhari ya bar Tinubu da aiki a Aso Villa Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Ayodele Fayose/Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Fayose ya ce Muhammadu Buhari ya kawo ci-baya

Tsohon gwamnan na jihar Ekiti yana ganin tsohon shugaban Najeriyan ya jawowa Najeriya ci-bayan tsawon shekaru 50 a mulkinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayo Fayose yake cewa gyara zai yi wa sabuwar gwamnatin APC wahala saboda irin barnar da aka tafka kafin Bola Tinubu ya karbi mulki.

Fayose yana neman kujera a mulkin Tinubu?

‘Dan adawan ya sake nanata bai bukatar mukami a gwamnatin APC da Tinubu duk da ana canza gwamnati aka gan shi cikin Aso Villa.

‘Dan siyasar yake cewa ko da shugaba Tinubu yana da niyyar yin gyara, zai gamu da kalubale musamman wajen biyan bashin da aka ci.

Jagoran na jam’iyyar PDP yake fadawa tashar akwai bashin kudin da aka karbo wanda sai nan da shekaru 50 gwamnati za ta fara biya.

Kara karanta wannan

Matakin Tinubu 1 ya jefa Najeriya cikin wahala Inji Sakataren Gwamnatin Buhari

Fayose ya ce ‘ya ‘ya da jikokinsu za a bari da nauyin kudin da aka aro a lokacin Buhari wanda ya jawo bashin kasar ya kai kusan N80tr.

Ana so shugaba Tinubu ya daina yabon Buhari

Shawarar tsohon gwamnan ga Tinubu ita ce Mai girma shugaban ya daina yabon Muhammadu Buhari, yana cewa ya bautawa kasa.

Idan sabon shugaban Najeriyan yana fitowa yana jinjinawa mulkin Buhari, Fayose ya ce wannan zai kawo rudani ne a tsakanin jama’a.

A maimakon a yabi Buhari, ‘dan adawan yana ganin abin da ya fi dacewa shi ne a nunawa Buhari kauna, a kai masa ziyara, a gode masa.

Shawarar Atiku ga gwamnatin Tinubu

A rahoton nan, an ji yadda Atiku Abubakar ya fadawa Bola Tinubu cewa shugaban Argentina zai yi koyi da shi domin a gyara Najeriya.

Atiku Abubakar ya zargi sabon shugaban kasar da cigaba da facaka da dukiyar gwamnati a lokacin da kasa ta shiga matsin lamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel