Yaron Tinubu Ya Ji Babu Dadi Daga Rokon Mutane a Kara Hakuri da Gwamnatin Mahaifinsa

Yaron Tinubu Ya Ji Babu Dadi Daga Rokon Mutane a Kara Hakuri da Gwamnatin Mahaifinsa

  • Folashade Tinubu-Ojo ta roki mutanen Najeriya suyi hakuri da gwamnatin Bola Tinubu duk da wahalar da al’umma suke ciki
  • Diyar shugaban kasar ta ce a sauran kasashen duniya, duk ana fuskantar irin abubuwan da ke faruwa a kasar nan a yanzu
  • Shi ma Seyi Tinubu ya ce wajibi ne jama’a su jure kuncin da aka shiga muddin ana so a ji dadin rayuwa sosai a kasar nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Folashade Tinubu-Ojo wanda diya ce a wajen Mai girma Bola Ahmed Tinubu ta yi kira ga mutane su kara hakuri da gwamnati.

Folashade Tinubu-Ojo kamar yadda The Cable ta rahoto, tayi wannan kira ne a wajen maulidin da Aljamahatul Qadiriyyah suka shirya.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi yadda Tinubu ya haddasa tashin Dala da rugujewar tattali a wata 8

Seyi Tinubu
Seyi Tinubu da iyalin shugaban kasa Hoto; Getty Images/SeyiTinubu (Instagram)
Asali: UGC

Diyar shugaba Tinubu tayi kira ga mutane

‘Yan kungiyar addinin musuluncin sun yi taron maulidin Annabi Muhammad SAW a Legas, sai aka gayyaci Madam Folashade Tinubu-Ojo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarinyar shugaban kasar ta fadawa mahalarta taron cewa duniya ce gaba daya ta ke fuskantar matsalar tattalin arziki ba Najeriya ba.

Duk da kukan wahalar da ake yi, Iyaloja din ta aikawa al’umma sako cewa su kara hakuri.

Jawabin Folashade Tinubu-Ojo a Maulidi

"Sakona ga daukacin ‘yan Najeriya shi ne don Allah su kara hakuri kadan. Komai zai dawo daidai; komai na lokaci ne,
Dole mu cigaba da sa rai. Tattali ya ruguje a fadin duniya, ba a Najeriya kadai ba ne. Muna addu’a Allah SWT ya cece mu.”

- Folashade Tinubu-Ojo

Seyi Tinubu ya kira ruwa a Instagram

Shi kuwa Seyi Tinubu wanda shi ne babban yaron shugaban kasar ya sake tsokano fushin jama’a da ya yi irin kiran nan a Instagram.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda Gwamnatin Buhari ta ‘saida’ man shekaru masu zuwa

Seyi Tinubu yake cewa mutane suna bukatar su jure halin da ake ciki domin gaba tayi kyau.

"Babu dadi ganin mutanen kasar nan suna shan wahalar da ya kamata a sha shekarun baya."
"Na so a ce ba a fama da wahalhalun da ake ciki a yau. Dole mu jure idan mu so gaba tayi kyau."

- Shugaban kasa

Matashin ya dauko kalaman nan ne daga jawabin da shugaban kasar ya yi can kwanaki.

Tun da Seyi ya yi maganar a dandalin sada zumuntar, mutane da-dama sun fito sun yi masa kaca-kaca yayin da ake zanga-zanga a wurare.

Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya

Rahoto ya zo cewa Bola Tinubu ya amince da kafa kwamiti na musamman domin yaƙi da miyagun ayyuka a manyan makarantu.

Tinubu ya naɗa Suleiman Kazaure wanda tsohon shugaban hukumar NYSC ne ya rike kwamitin bayan dawowa daga Addis Ababa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel