Sanatan Arewa Ya Tsarge Ministan Kudi da Gwamnan CBN da Ya Soki Manufofin Tinubu a Bidiyo

Sanatan Arewa Ya Tsarge Ministan Kudi da Gwamnan CBN da Ya Soki Manufofin Tinubu a Bidiyo

  • Sani Musa ya yi dogon jawabi da kwamitin tattalin arziki ya zauna da ministocin tarayya da gwamnan bankin CBN a majalisar dattawa
  • Sanatan ya soki yadda abubuwa su ke tafiya, yake cewa tsare-tsaren kudi da tattalin arziki da aka fito da su ba su kawo wani cigaba ba
  • ‘Dan majalisar yana mamakin yadda har yau ake cikin halin jiya-i-yau duk da bashin da aka karbo da kuma karya darajar Naira da aka yi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A kwanakin da suka gabata, majalisar dattawa ta gayyaci manyan jami’an gwamnatin tarayya da ke rike da tattalin arzikin Najeriya.

A wani bidiyo da Dele Momodu ya wallafa a dandalin Instagram, an ji wani dogon jawabi da Sanata Sani Musa ya yi gaban kwamitin majalisar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda Gwamnatin Buhari ta ‘saida’ man shekaru masu zuwa

Sanata
Sanata Sani Musa da Bola Tinubu a Majalisa Hoto: @MohdSaniMusa/@NgrSenate
Asali: Twitter

Majalisa ta gayyaci CBN da Ministoci

Maganganun Sanatan na Neja ta gabas a majalisar dattawa sun ja hankali ganin yadda ya a baya ya ce Bola Tinubu ya dace da rike Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Sani Musa ya nuna dole Bola Tinubu ya canza salon da yake kai domin manufofinsa ba su kawo cigaban tattalin arziki a kasar ba.

Sanata bai gamsu da karya Naira ba

A ra’ayin ‘dan majalisar, babu wata kasar kirki da za ta saki darajar kudinta ya rika yawo a kasuwa kamar yadda sabon gwamnan CBN ya yi.

Wajen zaman ne Sanatan ya tabo zancen bashin $3.3bn da aka karbo domin daidaita farashin Dala wanda yau ake saida ta a fiye da N1500.

Ina kudi da bashin da Najeriya ta karbo?

Majalisar dattawa tayi ta ba gwamnatin tarayya damar karbo aron kudi, ‘dan siyasar yana ganin ba za a ce ga abin da aka yi yau da bashin ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

Bangare mafi muhimmanci a wajen sa shi ne harkar gona wanda yake ganin manufofin gwamnati ba su taimakawa sha’anin noma ba.

Duk da matakan da aka dauka, ‘dan majalisar na Neja ya nemi Ministan kudi, Wale Edun ya yi masa bayanin masu hannun jarin da aka kawo.

An tabo NNPCL, NASENI a majalisa

Musa ya bada misali da NASENI da aka ba damar cin bashi da nufin inganta fasahar samar da lantarki daga rana amma har yau babu labari.

Jawabin Sanatan ya tabo halin da NNPCL ta ke ciki, ya nemi jin ina aka kwana a kan batun titunan da kamfanin man yake ginawa a kasar.

Cikin shawarwarin da ya bada shi ne ayi koyi da kasar Brazil wajen noma sannan a jawo kamfanoni irinsu Toyota su kafa kamfanins a Najeriya.

Mansur Sokoto ya yi tir da tsarin Tinubu

Ana da labari Sheikh Mansur Sokoto ya nuna ba taskance kaya a rumbuna ne ya haifar da tsadar abinci da hauhawar farashi a kasuwa ba.

Malamin yake nuna ba abinci ne kadai ya yi tsada a kasuwa har da sauran abubuwa kamar fetur, ya alakanta labarin da karya kimar Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng