'Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Daban da Ake Nema Ruwa a Jallo, Bayanai Sun Fito

'Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Daban da Ake Nema Ruwa a Jallo, Bayanai Sun Fito

  • Alamu sun nuna cewa rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta samu nasarar halaka shugaban ƴan daban da ake nema ruwa a jallo a jihar
  • Ƴan sandan sun samu wannan nasarar ne a wani samame ta sama da ta ƙasa da suka kai a maɓoyar ɗan daban wanda a baya ya halaka DPO na ƴan sanda
  • Wani babɓan jami'in ƴan sanda ya bayyana cewa an yi wa ɗan daban harbi da dama a jikinsa yayin samamen da ƴan sandan suka kai a maɓoyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Wataƙila ƴan sanda a jihar Rivers sun samu gagarumar nasarar halaka gagarumin ɗan daba mai suna Gift Okpara wanda aka fi sani da 2Baba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutane da dama sun rasu a wani mummunan hatsarin mota

2Baba ana zarginsa ne dai da kisan wani jami'in ƴan sanda (DPO), Bako Angbashim, cewar rahoton jaridar The Nation.

'Yan sanda sun sheke 2Baba
'Yan sanda sun halaka 2Baba da ake nema ruwa a jallo Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Hakan ya biyo bayan wani samame ta ƙasa da ta sama da jami’an tsaron haɗin gwiwa suka kai maɓoyarsa da ke Idu-Ekpeye da ke ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas a ranar Asabar da yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun harbi 2Baba

Jaridar The Punch ta ce wani babban jami’in ƴan sanda da ya nemi a sakaya sunansa domin ba shi da izinin yin magana a kan samamen, ya bayyana hakan.

A kalamansa:

"An yi wa 2Baba harbi da dama tare da wasu masu yi masa biyayya.
"Ya faɗi ƙasa, amma da sauri wasu yaransa suka ɗauke shi. Ƴan sanda na ci gaba da shiga dajin domin ɗauko gawarsa."

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, domin tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ba ta dawo da amsar saƙon da aka tura mata ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke rikakkun masu sace yara a Arewacin Najeriya, bayanai sun fito

Ƴan Sanda Sun Ragargaji Ƴan Bindiga a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Sokoto sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a jihar.

Jami'an ƴan sandan sun halaka wani ɗan bindiga tare da cafke wasu mutum 15 a yayin samamen da suka kai lokuta daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel