Jerin Sanatoci 45 da Aka Zaba Domin Aikin Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki a Majalisa
- An kafa kwamiti na musamman wanda za a ba alhakin aikin yin gyara a kundin tsarin mulkin Najeriya a majalisar dattawa
- A ranar Laraba, shugabanmajalisar dattawan kasar nan, Godswill Akpabio, ya sanar da wannan cigaba da aka samu a Abuja
- Kamar yadda Sanata Godswill Akpabio ya yi bayani, an zabi Sanata da zai wakilci kowace jiha, sai kuma aka kara wakili a yanki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Majalisar dattawa ta kafa wani kwamitin mutum 45 wanda zai yi aikin gyara da kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasa.
The Cable ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa na kasa, Godswill Akpabio, ya sanar da haka yayin zaman ranar Larabar nan.
Jibrin zai rike kwamitin kwaskwarima a Majalisa
Godswill Akpabio ya ce mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin zai shugabanci kwamitin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar yake cewa akwai bukatar ayi wa tsarin mulkin da ake amfani da shi garambawul saboda sauyin da ake samu.
Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya ce lokaci ne yanzu da ake ganin canji a duniya musamman ta fuskar kimiyya da fasaha.
Majalisar tarayyar ta na so dokokin Najeriya su zama daidai da zamanin da ake ciki a yau.
Yadda aka zakulo Sanatocin a Majalisa
A matsayinsa na wanda zai jagoranci aikin, Barau Jibrin zai gayyaci shugabannin majalisun dokokin jihohi, ya tattauna da su.
Tribune ta ce an zakulo ‘yan kwamitin ne daga kowace jiha, sannan aka kara hada da wakili daga kowane yanki da kuma Abuja.
A kowace jiha an dauki Sanata guda ne, idan an samu kari shi ne wanda zai wakilci yankinsa, a haka aka tara mutane har 45.
Shugaan majalisan ya ce babu wata jam’iyya ko shiyya da aka manta da shi a kwamitin.
Sunayen Sanatocin da ke kwamitin
1. Barau Jibrin
2. Opeyemi Bamidele
3. Oyelola Ashiru
4. Ali Ndume
5. Nwebonyi Onyeka
6. Abba Moro
7. Osita Ngwu
8. Oyewunmi Olalere
9. Sani Hanga
10. Enyinnaya Abaribe
11. Binus Dauda Yaroe
12. Bassey Etim Akpan
13. Ifeanyi Ubah
14. Abdul Ningi
15. Seriake Dickson
16. Agom Jarigbe
17. Ned Nwoko
18. Adams Oshiomole
19. Danjuma Goje
20. Osita Izunaso
21. Abdulhamid Ahmed
22. Khalid Mustapha
23. Sani Rufai
24. Mutari Dandutse
25. Yahaya Abdullahi
26. Natasha Akpoti-Uduaghan
27. Adebule Oluranti
28. Ugodiya Akwashiki
29. Sani Musa
30. Adeola Olamilekan
31. Adeniyi Ayodele
32. Abdulfatai Buhari
33. Simon Lalong
34. Aliyu Wamako
35. Shuaibu Lau
36. Ahmed Lawan
37. Sahabi Alhaji Ya’u
38. Ireti Kingigbe
39. Ipalibo Banigo
Sanatoci masu wakiltar yanki
40. Adamu Aliero (Arewa maso yamma)
41. Orji Uzor Kalu (Kudu maso gabas)
42. Francis Fadahunsi (Kudu maso yamma)
43. Bomai Mohammed (Arewa maso gabas)
44. Barinada Mpigi (Kudu maso kudu)
45. Umar Sadiq Sulaiman (Arewa maso tsakiya)
Kiran PDP ga Gwamnatin Tinubu
Muddin Bola Tinubu bai tashi tsaye ba, an ji labari Gwamnonin PDP sun ce Najeriya za ta bi tafarkin kasar Venezuela ta fuskar tattalin arziki.
Venezuela kasa ce mai arziki amma sai ga shi ana fama da rushewar tattali, Bala Mohammed ya ce Najeriyata kama wannan hanya a yau.
Asali: Legit.ng