Abba Kabir-Yusuf: Dan Takarar Gwamnan NNPP Da Ya Kwace Kano Daga Hannun APC

Abba Kabir-Yusuf: Dan Takarar Gwamnan NNPP Da Ya Kwace Kano Daga Hannun APC

  • Abba Kabir Yusuf, dan takarar NNPP a zaben gwamnonin 2023 a Kano, ya yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Kano
  • Ma su sharhin siyasa na ganin Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP na gaba da jam'iyya mai mulki ta APC in aka yi la'akari da zaben shugaban kasa da ya gudana a jihar
  • Kabir Yusuf ya taba rike kwamishina a jihar ya kuma yi takara da gwamna mai ci a 2019 inda aka kada shi

Abba Kabir Yusuf ne dan takarar NNPP a zaben gwamnoni da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris a Kano.

A sakamakon karshe da aka fitar, baturen zabe, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim, ya ce Yusuf ya samu kuri'u 1,019,602 yayin da dan takarar APC, Nasir Yusuf Gawuna ya samu kuri'u 890,705, inda ya zo na biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo

Abba Kabir
Abba Kabir-Yusuf: Sadu Da Dan Takarar Gwamna Na NNPP Da Ka Iya Kada APC A Kano. Hoto: Photo Credit: Abba Kabir-Yusuf
Asali: Facebook

Bayan kammala sakamakon zaben, NNPP ta lashe kananan hukumomi 30, yayin da APC ta samu kananan hukumomi 14.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wadanda NNPP din ta ci akwai Rano, Rogo, Wudil, Karaye, Kibiya, Minjibir, Albasu, Gezawa, Garko, Tudunwa, Bunkure, Gabasawa da Ajingi.

Daga cikin wadanda APC ta lashe akwai Shanono, Kunchi, Makoda, Dambatta, Warawa, Kabo, Bagwai, Takai, da Tsanyawa

Me ya sa Abba Kabir Yusuf zai iya lashe zaben

Masu sharhin siyasa a Jihar Kano na ganin sirikin jagoran NNPP na kasa kuma dan takarar shugabancin kasa a zaben da ya gudana na shugaban kasa da yan majalisar tarayya, Rabiu Kwankwaso, zai lashe zaben gwamnan.

Dalilin shi ne Kano, karkashin mulkin APC kusan shekara takwas, an ga sauye-sauye na siyasa da dama a zaben shugaban kasa, inda Kwankwaso ya samu kuri'a kusan miliyan daya yayin APC ta yi na biyu da tazara mai yawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: PDP ta yi jana'izar APC, ta lashe kujerar majalisa ta farko a jihar APC a Arewa

Kabir Yusuf ya yi takara da gwamna mai ci Abdullahi Ganduje a zaben 2015 karkashin inuwar jam'iyyar PDP amma ya sha kayi a zaben da ake ganin akwai kura-kurai da yawa.

Wasu abubuwan da ya kamata a sani game da dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar NNPP

An haifi mai fatan lashe gwamnan ranar 5 ga watan Janairu, 1963, a garin Gaya da ke karamar hukumar Gaya a Jihar Kano.

Ya yi makarantar firamare a firamaren Sumaila sai kuma ya wuce makarantar sakandire da ke karamar hukumar Gumel, da ke Jigawa a yanzu.

Kabir Yusuf ya na da babbar diploma ta kasa a bangageren kimiyyar kera manyan gine-gine (Civil Engineering) daga Kaduna Polytechnic kafin wuce jami'ar Bayero don yin diploma ta musamman a bangaren gudanarwa (Management) da kuma digiri na biyu a bangaren tafiyar da kasuwanci (Business Administration) daga jami'ar Bayero University, Kano.

Ya taba rike kwamishinan ma'aikatar ayyuka, gidaje da sufuri a Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Lashe Karamar Hukuma Ta Farko Da Tazara Mai Girma

Muhimman abubuwa 10 dangane da Dr Nasiru Yusuf Gawuna Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

A wani rahoto mai kama da wannan, Legit.ng ta kawo muku muhimman bayanai dangane da dan takarar gwamna na jihar Kano karkashin jam'iyyar APC, Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Gawuna, gogaggen dan siyasa ne wanda ya yi aiki da gwamnatoci uku a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel