Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Makudan Kudaden da Aka Sace a Karkashin Gwamnatin APC

Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Makudan Kudaden da Aka Sace a Karkashin Gwamnatin APC

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta sake caccakar gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Jam'iyyar ta yi caccakar ne yayin da take mayar da martani kan zargin da APC taɓyi na cewa jam'iyyun adawa ke ɗaukar nauyin zanga-zanga
  • PDP ta kuma zargi shugabannin APC da jami'an gwamnatinta da wawushe N20trn a cikin shekara takwas

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta ce ƴan Najeriya sun shaida yadda shugabannin jam’iyyar APC suka wawure sama da Naira tiriliyan 20.

PDP ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakinta, Debo Ologunagba, wacce Legit Hausa ta samu a yammacin ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnan PDP da salwantar da N144bn, ta kawo hujja

PDP ta caccaki gwamnatin APC
Jam'iyyar PDP na musayar yawu da jam'iyyar APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Idan dai za a iya tunawa, bisa hauhawar tashin farashin kayayyaki, wasu ƴan Najeriya a Minna, jihar Neja, da Kano, sun fito kan tituna suna zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani APC ta ce ƴan adawa ne suka yi ɗauka nauyin zanga-zangar.

PDP ta yi martani mai zafi kan gwamnatin APC

Da take mayar da martani kan martanin APC, PDP ta yi zargin cewa jam'iyyar mai mulki tana "ƙoƙarin siyasantar da wahala".

Wani ɓangare na sanarwar PDP na cewa:

"Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da mugun yunƙurin da fadar shugaban ƙasa Tinubu da jam’iyyar APC suka yi na sanya siyasa a zanga-zangar da ƴan Najeriya ke yi na nuna rashin amincewa da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da kuma tabarbarewar rashin tsaro a ƙasar nan sakamakon manufofin kyamar jama’a da ba a taba ganin irinsa ba da cin hanci da rashawa na gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin matsi a Najeriya, Remi Tinubu ta fadi lokacin da sauki zai zo

"Matakin da jam’iyyar APC ta ɗauka na barazana ga ƴan Nijeriya kan yadda suke amfani da ƴancinsu na dimokuradiyya da tsarin mulkin ƙasa na yin zanga-zangar adawa da rashin iya mulki, raɗaɗin talauci, yunwa, kashe-kashe da sauran abubuwan da suka faru a gwamnatin Tinubu, ya nuna cewa APC ba ta damu da halin ake ciki a ƙasar nan ba.
"Wannan salon da APC ta bi maimakon ta saurari jama'a, ba kawai tada hankali ba ne, illa kawai tura ƴan Najeriya bango.
A yau al’ummar Najeriya na neman kashe kansu yayin da dubban matasan mu ke tururuwa wajen barin ƙasar nan.
"Shin ba abin tada hankali bane cewa a cikin shekaru takwas da watanni tara da suka gabata, maimakon a riƙa tura dukiyar ƙasa domin inganta muhimman ababen more rayuwa a fagage masu fa’ida, ƴan Najeriya sun shaida yadda shugabannin jam’iyyar APC da jami’anta a gwamnati suka sace sama da Naira Tiriliyan 20.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke babban malamin addini a Najeriya, ta fadi laifinsa

Amfanin Cire Tallafin Man Fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan Tinubu ya fadi tarin amfanin da ke cikin cire tallafin man fetur a ƙasar nan.

Ministan na harkokin yaɗa labarai, Mohammed Idris ya ce da kuɗaɗen da ake samu bayan cire tallafin ne ake amfani da su wurin ayyukan raya ƙasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng