Kano: Gwamna Abba Ya Maida Martani Ga Ganduje Kan Roƙon Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

Kano: Gwamna Abba Ya Maida Martani Ga Ganduje Kan Roƙon Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

  • Gwamna Abba na Kano ya mayar da martani kan kokon barar da Ganduje ya aike masa na ya bar NNPP ya koma jam'iyyar APC
  • A wurin taron masu ruwa da tsaki, Ganduje ya roki gwamnan Kano da NNPP su aje komai a gefe, su taho zuwa APC mai mulkin ƙasa
  • Sunusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan Kano ya ce Ganduje ya fi kowa sanin hanyar aika saƙo ga Abba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya maida martani kan goron gayyatar da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya aike masa tare da muƙarrabansa.

Gwamna Yusuf, wanda ya yi magana ta bakin kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Ganduje bai biyo hanyar da ta dace ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya yi magana kan yiwuwar Kwankwaso ya koma jam'iyyar APC su sake haɗuwa

Gwamna Abba ya mauda martani ga Ganduje.
"Sakon Gayyatarka ba ta biyo hanyar da ta dace ba" Gwamna Abba ga Ganduje Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, a wurin taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC na Kano ranar Alhamis, Ganduje ya roƙi Gwamna Abba ya baro NNPP, ya shigo APC mai mulkin ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

BBC Hausa ta ruwaito Ganduje ya ce:

"Muna kira ga duk wanda ke son shiga APC ya taho, musamman muna gayyatar gwamnan jihar Kano da NNPP su taho mu haɗe wuri ɗaya a APC."

Gwamna Abba ya maida martanin ga Ganduje

Amma da yake martani kan wannan ƙoƙon bara na Ganduje, Gwamna Yusuf ta bakin Dawakin Tofa ya ce:

"Mun ji labarin yana roƙon gwamna ya koma APC, amma abin mamakin a matsayinsa na tsohon gwamna kuma tsohon mataimakin gwamna ya fi kowa sanin hanyar da ake tura saƙo ga gwamna mai ci.
"Mai girma Gwamna ba shi na wani shiri na barin jam'iyyarsa kuma ba zai barta ba. Sauya sheƙa a siyasa kamar canza gida ne, ba zai iyu ka wayi gari kawai ta haɗa kayanka ka ce na bar jam'iyyata ba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da za su faru da NNPP da APC idan Abba, Kwankwaso suka sauya-sheka

"Akwai abubuwan da ya kamata ka yi kafin ka sauya gida, don haka wannan goron gayyata a sama muka ji ta kuma a nan muka barta."

Wani mamban NNPP a Kano ya shaida wa Legit Hausa cewa ba su goyon bayan Abba da Kwankwaso su koma jam'iyyar APC.

Ɗan Kwankwasiyyan ya ce matuƙar suka zaɓi komawa APC to da yawan mazauna Kano ba zasu ƙara zaɓensu ba saboda yadda aka dawo daga rakiyar Ganduje.

Ya ce:

"Wallahi har bana son jin wannan labarin, ina tare da Kwankwaso duk inda ya koma amma ba na kaunar ya shiga APC. Ka duba yadda aka tsani Ganduje, zamu jira muga abinda zai faru."

Gwamnatin Kebbi ta tsige hakimai 3

A wani rahoton kuma Hakimai uku sun rasa rawaninsu a jihar Kebbi kan laifukan da suka haɗa da lashin ladabi, rashin ɗa'a da wasu guda biyu.

Gwamnatin jihar karkashin Gwamna Nasir Idris ta sanar da haka bayan kammala bincike kan laifukan da ake zargin hakiman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel