Gwamnan Arewa Ya Tuɓe Rawanin Hakimai 3, Ya Kore Su Daga Aiki Kan Wasu Dalilai 4

Gwamnan Arewa Ya Tuɓe Rawanin Hakimai 3, Ya Kore Su Daga Aiki Kan Wasu Dalilai 4

  • Hakimai uku sun rasa rawaninsu a jihar Kebbi kan laifukan da suka haɗa da lashin ladabi, rashin ɗa'a da wasu guda biyu
  • Gwamnatin jihar karkashin Gwamna Nasir Idris ta sanar da haka bayan kammala bincike kan laifukan da ake zargin hakiman
  • Ta ce sun aikata abubuwan da suka saɓa wa kundin dokokin aikin gwamnati na jihar Kebbi wanda hukuncinsu kora ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ta sanar da korar hakimai uku a kananan hukumomi uku a jihar.

Gwamnatin ta tsige waɗannan hakimai ne bisa zarginsu da aikata laifuka huɗu da suka haɗa da rashin ɗa'a, rashin ladabi ga na gaba, nuna ɓangaranci da barin wurin aiki.

Kara karanta wannan

An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa

Gwamna Nasir Idris Kauran Gwamdu.
Gwamnatin Kebbi Ta Kori Hakimai Uku Daga Kan Karagar Mulkin Kan Dalilai Hoto: Dr. Nasir Idris
Asali: Facebook

Shugaban hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi ta jihar Kebbi, Alhaji Mansur Shehu ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa, Shehu ya bayyana cewa wannan matakin ya yi daidai da tsari da tanadin kundin dokokin ma'aikatan gwamnati (PSR).

Jerin hakiman da aka warware rawaninsu

Hakiman da gwamnatin ta tsige daga karagar mulki sun haɗa da, Alhaji Lawal Yakubu, Mai Arewan Yeldu a ƙaramar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

Sauran sune, Malam Ahmed Sani, Sarkin Gabas Geza a ƙaramar hukumar Dandi da kuma Alhaji Tukur Aliyu, Jagwadejin Bakuwe shi kuma a karamar hukumar Suru.

Dukkan hakimai uku da wannan matakin kora ya shafa suna ƙarƙashin masarautar Gwandu a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, Daily Post ta ruwaito.

Shin gwamnati ta yi bincike kan laifukan hakiman?

Kara karanta wannan

Gwamna Abba, Sule da wasu gwamnoni 7 da suka shirya zartar da hukuncin kisa kan masu garkuwa

Ya ce bayan gudanar da bincike da tattautawar da ta dace, hukumar ta gano cewa hakiman 3 sun cancanci a kore su daga aiki bisa la'akari da dokar ma’aikata ta PSR 030302.

Laifukan da aka gano sun aikata sun haɗa da rashin ɗa'a wanda ya saɓawa doka ta PSR 030301 da barin wurin aiki ba tare da izini ba wanda ya saɓawa PSR 030302 & 030407.

Atiku ya taya gwamnoni 2 murna

A wani rahoton na daban Alhaji Atiku Abubakar ya aike da saƙon taya murna ga gwamnonin PDP 2 da suka yi nasara a kotun ƙoli yau Alhamis.

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Fubara na Ribas da Gwamna Kefas na Taraba a zaben 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel