Zaben 2027: Jigon PDP Ya Bayyana Dalili 1 da Ya Sanya Hadaka Ba Za Ta Yi Aiki a Kan APC Ba
- Segun Showunmi ya bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta iya kayar da shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ba tare da yin haɗaka ba
- Jigon na PDP ya bayyana cewa tsarin haɗakar da jam’iyya mai mulki ta yi amfani da shi a 2015 mai yiwuwa ba zai yi wa ƴan adawa aiki ba a 2027
- Tsohon ɗan takarar gwamnan a jihar Ogun ya ce PDP na buƙatar gyara jam’iyyar a cikin gida ne kawai, kuma za ta kayar da jam’iyya mai mulki cikin kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Ogun kuma jigo a jam’iyyar PDP, Segun Showunmi, ya bayar da dalilan da ya sa jam’iyyar haɗaka ba za ta iya yin aiki a 2027 kan APC ba.
A wata hira da jaridar Punch ta buga a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu, jigon na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa dabarun da APC ta yi nasarar kawar da PDP a 2015, ba su nuna cewa za su yi wa ƴan adawa aiki a 2027 ba.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Suna tunanin za su iya amfani da abin da maƙiyansu suka yi amfani da su wajen kayar da su, su ma su kayar da su, a lokacin da maƙiyansu suka so su doke su, kimiyya ta ce haɗewar za ta yi kyau kuma an yi haka ne da jam’iyyar Shugaba Tinubu ta ACN da jam'iyyar CPC ta Buhari.
"Wasu ƴaƴan jam’iyyar PDP ma sun fice ne domin shiga wannan haɗewar, sun cutar da kansu saboda da yawa daga cikinsu sun dawo jam’iyyar a yanzu."
"Masu tunanin wannan manufar malalata ne” - Segun Showunmi
Jigon na PDP ya bayyana waɗanda suka fara haɗakar a matsayin malalata, maimakon yin tunani da nemo hanyoyin da za a bi don kawar da APC.
Showunmi ya bayyana cewa jam’iyyun siyasar da ake sa ran za su yi wannan haɗaka duk suna da ƴan takara da su ma ke son zama shugaban ƙasa, kuma zai yi wuya su haƙura da muradinsu.
A kalamansa:
"Za su shafe shekaru 20 masu zuwa suna fafutuka da kuma yaƙar kansu kan wanene zai zama shugaban ƙasa domin dukkansu suna son zama shugaban ƙasa a lokaci guda."
Jigo a jam’iyyar PDP wanda ya tabbatar da sha’awarsa ta neman kujerar shugaban jam’iyyar ya buƙaci cewa dole ne su haɗa kai, su warware saɓanin da ke tsakaninsu, su gyara jam’iyyar a cikin gida don samun damar doke APC ba tare da haɗewa da wata jam’iyyar siyasa ba.
A cewarsa:
"Mun sha kaye a zaɓe, amma hakan ba yana nufin ba za mu sake yin nasara ba da zarar mun duba cikin gida muka gyara kura-kuranmu."
Showunmi Ya Ziyarci Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa Segun Showunmi ya kai wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ziyara a gidansa da ke Daura.
Showunmi wanda na hannun daman Atiku Abubakar ne ya sanar da ziyarar ta sa ga Buhari a shafinsa na X.
Asali: Legit.ng