Kotun Koli: Kwankwaso Ya Fadi Abubuwa 2 da Abba Zai Tunkara Tun da Ya Samu Nasara

Kotun Koli: Kwankwaso Ya Fadi Abubuwa 2 da Abba Zai Tunkara Tun da Ya Samu Nasara

  • ‘Inganta ilimi da tsaro muka sa a gaba yanzu’ a cewar Rabiu Musa Kwankwaso a kan gwamnatin Kano
  • Tsohon gwamnan wanda yanzu ya zama cikin ‘yan bada shawara yana fatan NNPP za ta kawo cigaba
  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ce Abba Kabir Yusuf zai bunkasa ilmi, inganta tsaeo kuma zai kawo ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya zanta da ‘yan jarida bayan an tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halataccen gwamnan Kano.

Sanata Rabiu Kwankwaso wanda shi ne jagoran NNPP da ya kai jam’iyya mai alamar kayan dadi ga nasara, ya ji dadin hukuncin kotun.

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso
Gwamnan Kano tare da Rabiu Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A hirar da TRT Hausa tayi da ‘dan siyasar Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnatin NNPP za ta dukufa wajen yi wa mutanen jihar Kano aiki.

Kara karanta wannan

Idan Kwankwaso Ya Ce Magoya Bayansa Su Faɗa Wuta, Rabin Kano Za Su Faɗa Wutan, in Ji Galadima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Menene a gaban Abba yanzu?

Bayan samun nasara, tsohon Sanatan na Kano ya ce abin da ke gaban gwamnatin Abba shi ne yin ayyukan da za su taimakawa al’umma.

Kwankwaso ya ce babban abin da ake ba muhimmanci a tsarin Kwankwasiyya shi ne ilmi, kuma za a maida hankali a kan harkar a Kano.

Ganin an fara fama da matsalolin rashin tsaro, Kwankwaso wanda ya taba yin ministan tsaro ya ce Abba zai tabbatar da zaman lafiya.

Abin da Abba ya fadawa Kwankwaso

Ko a ranar da aka yi magana da shi, Kwankwaso ya ce Mai girma Abba ya fada masa irin tsare-tsaren da zai kawo domin cigaban Kanawa.

Wadannan tsare-tsare za su inganta tsaro, su bunkasa ilmi tare da kawo cigaba a Kano.

A cewar Kwankwaso wanda ya yi mulki sau biyu a 1999 da 2011, sai an samu tsaro za a iya noma da sauran sana'o'i har a iya ganin cigaba.

Kara karanta wannan

Kano: Bayan nasara a kotu, Gwamnatin Kano ta magantu kan masu niyyar wawushe asusun jihar

Gwamnatin Abba tana da shekaru 3

Madugun na Kwankwasiyya ya shaidawa gidan rediyon yana so gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta zama abin misali nan da shekaru uku.

Zuwa yanzu shekaru kusan uku suka rage a wa’adin NNPP, an dauki watanni a shari’ar zabe tsakaninsa da jam'iyyar Nasiru Gawuna.

Sanusi II a kan hukuncin kotun koli

Ana da labari Muhammadu Sanusi II ya fadawa APC ana karbar kaddara ne bayan zabe, ya ce jam'iyyar ta nemi karbe mulki da karfin tsiya.

Sarkin Kano na 14 yabi alkalan kotun koli da yin adalci wajen barin Abba Gida Gida a mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng