“Abin da Zai Faru a Zaben 2027 Idan Jam’iyyun Adawa Ba Su Hada Kai Ba”, Jigon PDP Ya Yi Hasashe

“Abin da Zai Faru a Zaben 2027 Idan Jam’iyyun Adawa Ba Su Hada Kai Ba”, Jigon PDP Ya Yi Hasashe

  • Daniel Bwala, jigon jam'iyyar adawa ta PDP ya ce dole sai jam'iyyun adawa sun hada kai za su iya kwace mulki a hannun Shugaba Tinubu
  • A cewar Bwala idan har jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyu ba su hada kai ba, to suna ji suna gani Tinubu zai yi tazarce a zaben 2027
  • Haka zalika, jigon PDP ya zargi Shugaba Tinubu da haddasa rikici a jam'iyyun adawa, inda ya buga misali da rikicin NNPP da na jihar Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani jigon jam'iyyar PDP, Daniel Bwala ya ce har sai jam'iyyun adawa sun hada kai ne za su iya kwace mulki hannun jam'iyyar APC a zaben 2017 idan ya zo.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a jam'iyyar PDP, Atiku da wasu gwamnoni sun fara takun saka mai zafi

Bwala ya bayyana hakan a ranar Talata a hirarsa da Channels TV, inda ya ce ma damar jam'iyyun ba su yi hadaka ba, Shugaba Tinubu zai yi shekara 8 a mulkin Najeriya.

Hanyar da jam'iyyun adawa za su karbi mulki daga hannun Tinubu a 2027
Daniel Bwala ya ce dole sai jam'iyyun adawa sun hada kai za su iya kwace mulki hannun Tinubu a 2027. Hoto: @officialABAT, @BwalaDaniel
Asali: Twitter

Muhimmancin hadakar jam'iyyun adawa a zaben 2027 - Bwala

A cewar Bwala:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ma madamar jam'iyyun adawa ba su hada kai ba, Tinubu zai yi shekara takwas, wannan tabbas ne."
"Dole sai jam'iyyun adawa sun zama tsintsiya madaurinki daya, wannan abin da na sani akai ke nan."

Jigon jam'iyar PDP ya kuma nuna bukatar da ke da akwai na jam'iyyun adawar su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu don yin nasara.

Tinubu na haddasa rikici a jam'iyyun adawa - Bwala

A tattaunawar, Bwala ya zargi Tinubu da haddasa rikici a jam'iyyun adawa, yana mai cewa shugaban ne ya haddasa rikicin da ya mamaye jam'iyyar NNPP, rahoton Osundefender.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sake yi wa jam'iyyar PDP lahani a arewa yayin da ake jiran hukuncin Kotun Koli

Ya buga misali da rikicin jihar Rivers, biyo bayan sabanin da aka samu tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike, Bwala ya ce Tinubu na da hannu a ciki.

Jigon PDP yayi hasashen cewa za a tsige gwamnan daga ofishinsa, inda ya kara da cewa ya shiga tarko ne, duk da bai fadi wanda ya dana wa gwamnan tarko ba.

Da kamar wuya a iya hambare APC a 2027, Rabiu Dahiru ya fadi dalili

Rabi U Dahiru, mazaunin garin Unguwar Dahiru da ke Funtua, jihar Katsina, ya ce da kamar wuya wata jam'iyyar adawa ta karbi mulki daga hannun APC a zaben 2027 mai zuwa.

Da ya ke zantawa da Legit Hausa, Malam Dahiru ya tariyo yadda zaben 2023 ya gudana, inda ya ce son abin duniya ya hana jam'iyyun adawar hada kansu, kuma suka sha kaye.

A cewarsa:

"Ba lallai ne shugabannin jam'iyyun su amince da yin 'maja' ba, saboda kowa son zuciya ta yi masa yawa, muna ji muna gani aka rinka raba taliya da naira dari biyar ana dangwala kuri'a.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya yi hasashen matsala ga PDP, ya bayyana babban gwammnanta da zai koma APC

"Sannan su wa ye suka bude kofar da Shugaba Tinubu ya yi nasara? Su din ne dai 'yan jam'iyyar adawar. Da yawansu sun yi wa APC aiki ta bayan fage, ga misalin Nyesome Wike nan."

Malam Dahiru ya yi ikirarin cewa ko raba in raba na kuri'un da aka samu a jihar Kano, shirin APC ne, "shi ya sa har ake kishin-kishin Tinubu zai ba Kwankwaso mukamin minista."

Shi ma a nasa ra'ayin, Kwamred Kamaluddeen Mukhtar, ya ce:

"Yadda PDP ta shafe shekaru 16 suna mulki ba tare da samun turjiya ba, haka APC za ta yi hakan ba tare da wata turjiya ba, Tinubu na da basira, har abokan adawa yake yi wa alheri.
"Siyasa a duniya ake amfana da ita, don haka babu wanda ba zai fita daga jam'iyyarsa ya bi APC ba ma damar ya san zai samu wani abu."

Yan bindiga sun sace miji da mata da karamin yaro a jihar Neja

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna kuma Sanata ya watsar da jam'iyyarsa zuwa APC, ya bayyana manyan dalilai

A wani labarin, a ranar Talata ne 'yan bindiga suka sake kai farmaki kauyen Garam, jihar Neja inda suka yi garkuwa da miji da mata da wani karamin yaro.

Ba wannan ne karo na farko da 'yan bindigar ke kai farmaki garin ba, ko a makon da ya gabata sai da suka kashe mutum daya tare da sace mutum uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel