Nazarin Shekarar 2023: Peter Obi, Kwankwaso da ‘Yan Siyasa 6 Da Suka Fi Kowa Tasiri a Shekarar 2023
- An yi babban zabe a bana wanda jam’iyyar APC ta samu rinjaye a karkashin jagorancin Asiwaju Bola Tinubu
- Akwai wasu ‘yan siyasan da aka gane karfinsu a shekarar nan ta 2023, duk da ba su yi nasarar lashe zabe ba
- Peter Obi da Rabiu Kwankwaso wanda su ka bar PDP, sun taimakawa LP da NNPP wajen samun kujeru rututu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Su wani ‘yan siyasan ne su ka nuna gwanintarsu a 2023:
1. Bola Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nuna shi gwarzo ne a siyasa da ya lashe zaben shugaban kasa a zuwan farko, abin da ba a taba yi ba sai a 2007.
Tinubu ya yi nasara wajen samun tikitin jam’iyyar APC mai-mulki, sannan ya doke kowa a babban zabe. Nakasarsa kurum ita ce ya rasa jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya shigo wannan jeri na fitattun ‘yan siyasan da su ka yi zarra a bana ne ba domin komai ba sai yadda ya lashe tikitin jam’iyyar PDP.
Wazirin Adamawa ya ba Nyesom Wike mamaki a zaben tsaida gwani. Watakila Aminu Waziri Tambuwal ya taimaka wajen canza lissafin siyasar.
3. Peter Obi
Peter Obi ya motsa kasa a zaben shekarar nan ta 2023. ‘Dan takaran shugabancin Najeriyan ya bada mamaki sosai bayan ficewarsa daga PDP a 2022.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya farfado da jam’iyyar hamayya ta LP, ta yi irin kokarin da ba a taba gani ba, musamman a kudancin Najeriya.
4. Rabiu Musa Kwankwaso
Shi ma Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP kuma ya nunawa ‘yan siyasa irin tasirinsa musamman a mahaifarsa ta Kano.
Jagoran na Kwankwasiyya ya zo bayan APC, PDP da LP ne a zaben shugaban kasa, amma NNPP ta samu mulkin Kano da kujerun ‘yan majalisu barkatai.
5. Aliyu Magatakarda Wammako
Ya kamata a jinjinawa Aliyu Magatakarda Wammako wanda ya jagoranci APC ta karbe mulkin jihar Sokoto da kujerar 'yan majalisu da yawa a 2023.
Tsohon gwamnan ya hana mataimakin gwamna a lokacin zama Sanata a PDP. Shakka babu an kara fahimtar tasirin Wammako a siyasar kasa.
6. Nyesom Wike
Nyesom Wike ya taimaka sosai wajen rusa takarar Atiku Abubakar. Shi ne ya jagoranci wasu gwamnonin PDP na G5 wajen ballewa daga jam’iyyar.
Saboda kokarin da ya yi a zaben 2023, Bola Tinubu ya ba shi kujerar Minista. A dalilin Wike, APC ta bada mamaki ta samu kuri’u fiye da 231, 000 a a Ribas.
Shari'ar zaben Kano a kotun koli
Nan da kwanaki za a san wanda ya yi nasara a shari'ar da ake yi a kan zaben Kano. Alkalai biyar su ka zauna a teburin kotun koli domin a raba gardama.
Ana da labari Inyang Okoro wanda ya yi hukunci a shari’ar Bola Ahmed Tinubu da PDP da LP a zaben 2023 ya jagoranci zaman da aka fara a makon nan.
Asali: Legit.ng