Buhari zai rabawa Tinubu, Osinbajo, da Amaechi gardama a APC kafin zaben fitar da gwani

Buhari zai rabawa Tinubu, Osinbajo, da Amaechi gardama a APC kafin zaben fitar da gwani

  • A watan Mayun 2022 ne jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben tsaida ‘dan takarar shugaban Najeriya
  • Ana tunanin shugaba Muhammadu Buhari ba zai bari APC ta shiga filin zabe ba tare da ya sa bakinsa ba
  • Shugaban kasar zai fayyacewa jam’iyyarsa wanda yake so ya samu tikitin takarar shugaban kasa a 2023

Abuja - A watan Mayun 2022 ne shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana wanda yake goyon bayan ya samu takarar kujerar shugaban kasa a APC.

Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu 2022. Hakan na zuwa ne a lokacin da aka shiga yakin neman takarar shugaban kasa.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa shugaban kasa yana duba ‘yan takarar da suka fito, yana nazarin tarihinsu da halayyarsu kafin ya yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

Idan Muhammadu Buhari ya kammala wannan, zai fada ko ya nunawa hadimansa inda ya sa gaba.

Da aka taba yi wa Buhari tambaya a kan zaben 2023, sai ya ce ba matsalarsa ba ce. A game da ‘dan takararsa kuwa, sai ya ce ba zai bari a san wanene shi ba.

Zaben APC ya karaso

A ranar 30 zuwa 31 ga watan Mayu mai zuwa ake sa ran jam’iyyar APC za ta shirya zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa, a san wanda zai rike tutar 2023.

Tinubu, Osinbajo, da Amaechi
Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Asiwaju Bola Tinubu Hoto: newsday.com.ng
Asali: UGC

Wani wanda yake aiki a fadar shugaban kasa ya ce Mai girma Muhammadu Buhari ba zai bari a shiga zaben fitar da gwanin ba tare da ya tsoma bakinsa ba.

Kamar yadda shugaban kasa ya shiga maganar zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa, majiyar ta ce haka zai yi don gudun neman tutan ya kawo rikici.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

“Shugaban kasa ya san halin wadanda suke takara, ya san tarihinsu, ya san abin da za su iya ko yadda za su tafiyar da kasa idan sun samu mulki.”
“Saboda haka ba zai taba bari a shiga filin zabe ba tare da ya fadi inda za a bi ba. Kun taba ganin shugaba da ke mulki bai damu da mahajinsa ba?”

- Majiya a fadar shugaban kasa

Kamar yadda gwamnoni ke yi a matakan jihohi, ana ganin Buhari ba zai bari ta fanjama-fanjam ba. Jaridar Sahara Reporters ta karfafi wannan labari a wani rahoto.

Ciwon kan da za ayi a APC

Shugaban Najeriyan zai yi zabi ne tsakanin mataimakinsa, Yemi Osinbajo, Ministocinsa; Rotimi Amaechi da Chris Ngige da kuma irinsu Asiwaju Bola Tinubu.

Sauran wadanda suke neman mulki a APC sun hada da Rochas Okorocha, Orji Uzor Kalu sai wasu gwamnonin jihohi masu-ci; Yahaya Bello da David Umahi.

Ana jita-jitar gwamnan Ekiti, Dr Kayode Fayemi; da gwamnan babban banki na CBN, Godwin Emefiele duk za su fito takara a jam’iyyar ta APC mai mulki.

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

'Yan takaran 2023 sun kai 40

A gefe guda kuma akwai Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Sanata Anyim Pius Anyim, Peter Obi, Aminu Tambuwal, Dr Nwachukwu Anakwenze a jam'iyyar PDP.

Ragowar sun hada da; Olivia Diana Teriela, Dele Momodu, Ayo Fayose, Muhammed Hayatu-Deen, Bala Mohammed, Udom Emmanuel da su gwamna Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel