Kwankwaso Ya Fara Kamfe Gadan-Dagan, Ya Ce APC da PDP Sun Kashe Kasa

Kwankwaso Ya Fara Kamfe Gadan-Dagan, Ya Ce APC da PDP Sun Kashe Kasa

  • Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabiu Kwankwaso ya kara caccakar APC da PDP kan mulkin Najeriya tsawon shekaru 24
  • Kwankwaso, mai neman zama shugaban kasa a inuwar NNPP ya fara kamfe gadan-gadan a arewa maso gabas
  • Dan takarar ya ce manyan jam'iyyun sun maida kasar nan baya ta kowane bangare, ya shawarci mutane su guje su a 2023

Bauchi - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya shawarci 'yan Najeriya su guji zaben wasu jam'iyu musamman APC da PDP a zaben watan Fabrairu.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kwankwaso ya baiwa yan Najeriya wannan shawarin ne a wurin Ralin kamfe dinsa na arewa maso gabas da ya gudana a Bauchi.

Kwankwaso a Bauchi.
Kwankwaso Ya Fara Kamfe Gadan-Dagan, Ya Ce APC da PDP Sun Kashe Kasa Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kwankwaso ya bayyana cewa akwai bukatar mutanen Najeriya su farga su fatattaki APC da PDP wadanda suka lalata Najeriya tsawon shekaru sama da 20.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso ya fadi yadda zai sauya tsarin JAMB, NECO da WAEC idan ya gaji Buhari

A kalamansa, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bari na yi amfani da wannan damar na gaya maku mutanen arewa maso gabas da ma Najeriya baki daya cewa jam'iyyarmu NNPP wuyanta ya kai tsara, mun shiga kowace gunduma a kasar nan."

APC da PDP sun kunyata kasar nan - Kwankwaso

Tsohon gwanman jihar Kano ya roki magoya bayan jam'iyyar NNPP su tashi tsaye su yi aiki tukuru domin damin nasara a watan Fabrairu.

A cewarsa, mulkin manyan jam'iyyu biyu watau PDP da APC da ya shafe shekaru 24 ya gaza mafi munin gazawa.

Karidar Ripples Nigeria ta rahoto dan takarar na cewa:

"Sun gaza tsinana komai a kasar nan kama daga bangaren tattalin ariziki, tsaro da manyan ayyukan raya kasa, sun gaza har a bangaren hada kan 'yan Najeriya."

Kwankwaso ya ce jam'iyyar NNPP ce kadai mafita game da kalubalen da suka dabaibaye Najeriya sakamakon gurbataccen shugabanci a tsawon waɗan nan shekaru.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

Tsohon gwamnan ya ce idan har 'yan Najeriya suka amince masa, gwamnatinsa zata tsawaita JAMB ta kai shekaru hudu kafin a daina amfani da ita.

APC ta karyata PDP a Zamfara

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Musanta Rahoton Cewa Hadiman Gwamna Matawalle Sun Koma PDP

Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta fayyace gaskiya game da rahoton da ake cewa manyan hadiman Matawalle sun sauya sheka zuwa PDP.

APC mai mulki ta ce mutanen da suka Koma PDP ba su da mukami a mulkin Bello Matawalle, a zaamanin mulkin tsohon gwamna ne suka rike SA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel