Dino Melaye Ya Sha Alwashin Ba Zai Kallubalanci Sakamakon Zaben Gwamnan Kogi Ba, Ya Bada Dalili

Dino Melaye Ya Sha Alwashin Ba Zai Kallubalanci Sakamakon Zaben Gwamnan Kogi Ba, Ya Bada Dalili

  • Sanata Dino Melaye ya rungumi kadara ya hakura da batun zama gwamnan jihar Kogi
  • Dan takarar gwamnan na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kogi ya ce ba zai tafi kotu ba domin kwato hakinsa
  • Ya bayyana cewa tuni ya dena yarda da bangaren shari'a, yana mai cewa bangaren shari'ar ta zama wani sashi ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Sanata Dino Melaye na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) dan takarar gwamna a jihar Kogi, ya ce ba zai tafi kotun zabe don kallubalantar nasarar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta sanar da Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Alkalan da suka yi kuskure a shari’ar zaben Kano za su yabawa aya zaki a Majalisar Shari’a

Sanata Dino Melaye
Dino Melaye shi ya zo na uku a zaben gwamnan jihar Kogi. Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

A ranar Laraba, Sanata Melaye, wanda ya zo na uku a zaben, ya jadada cewa a halin yanzu bangaren shari'a ba ta adalci, kuma ta zama wani sashi ne na APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Punch ta rahoto, Melaye ya ce:

"Yanzu bangaren shari'a ba itace gatar al'ummar kasa ba, ta zama wani sashi ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress. Me zai saka duk wani wanda ya san ciwon kansa ya tafi kotu duba da cewa APC ita ke juya bangaren shari'a?
"Na cire tsammani baki daya a bangaren shari'a."

Kotun Daukaka Kara ta dauki mataki mai tsauri kan karar neman korar gwamnan PDP, Kefas

A bangare guda, Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja za ta yanke hukuncinta kan karar da NNPP ta shigar na kallubalantar nasarar Gwamna Agbu Kefas a kotun zaben Taraba.

Kara karanta wannan

Farfesa Jega ya kawo hanyoyin da za a bi kafin a iya gyara hukumar INEC a Najeriya

Idan za a iya tunawa Kotun Daukaka Karar ta kori gwamnoni biyu na PDP, abin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar, ya yi suka a kai, ya kuma dora wa gwamnatin tarayya na APC laifi.

Gwamnonin na PDP sun ce suna da kwarin gwiwa a bangaren shari'a suka kuma ce suna fatan Kotun Koli za ta musu adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel