Shaibu: Na Shafe Watanni 6 Ba a Biyana Sisin Gwamnati a Matsayin Mataimakin Gwamna
- Philip Shaibu ya ce ya dauki watanni ba tare da turowa ofishinsa kudi ba saboda babu jituwa tsakaninsa da Gwamna
- Mataimakin gwamnan Edo ya yi rigima da Mai girma Godwin Obaseki, saboda haka ne aljihunsa ya yabawa aya zaki
- Kwamred Philip Shaibu yake cewa ya hakura da komai a gwamnati saboda jihar Edo ta zauna cikin kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya yi bayanin irin wahalar da yake sha yayin da yake kan kujerar mulki.
Mai girma Philip Shaibu ya yi bayanin yadda ya sadaukar da hakkokinsu domin cigaban jihar Edo, Vanguard ta kawo rahoton.
Mataimakin Gwamnan Edo ba ko sisi
Kwamred Philip Shaibu ya zargi Mai girma gwamna watau Godwin Obaseki da rike wasu kudin da ya kamata a turo ofishinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin gwamnan ya ce haka yake ta fama a tsawon watanni shida da su ka wuce a lokacin da rigimar mulki tayi kamari.
NUJ ta gayyato Philip Shaibu a Edo
Shaibu ya fadi wannan ne da aka kira shi domin gabatar da jawabi wajen bude sabon ofishin kungiyar NUJ a garin Benin a jiya.
A jawabin da ya yi ranar Talata gaban ‘yan jarida, Leadership ta ce Shaibu ya ce ya shiga siyasa ne domin kawo cigaba a Edo.
Ana da labarin cewa an samu mummunan sabani tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da Philip Shaibu saboda bambancinsu.
"Kun san akwai rigima tsakanina da gwamna. An yi watanni shida, babu kudin da aka turo zuwa ofishina.
Zan cigaba da jajircewa domin dole a samu hadin-kai a Edo, a kullum jihar Edo ya kamata ta zama a ranmu.
Na jajirce domin tabbatar da cewa an samu shugabanci na kwarai sannan dole a sa jihar Edo a kan gaba."
- Philip Shaibu
Mataimakin gwamnan yake cewa ya sallama duk wasu hakkokinsa kuma nan gaba zai kira ‘yan jarida domin ya shaidawa duniya.
Rigimar APC da NNPP a Kano
Ana da rahoto Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shiga kowace karamar hukuma da ake da ita a Kano, ya aika mata wasu jami’ai uku.
Wasu suna ganin an yi nadin wadannan jami’ai ne saboda wofantar da shugabannin kananan hukumomi 44 wadanda ‘Yan APC ne.
Asali: Legit.ng