Labari Mai Zafi: Kotun Koli Ta Tsaida Ranar Sauraron Shari’ar Zaben Gwamnan Kano
- Kotun koli ta sa rana domin a fara zama a game da shari’ar zaben gwamnan jihar Kano na 2023
- Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna za su san matsayarsu yayin da kotun koli ta tsaida ranar zama
- Alkalan da su ka saurari karar a kotunan baya duk rusa nasarar da INEC ta ba Abba Gida Gida
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bayan dogon jira da aka yi, Kotun koli ta sa ranar da za ta saurari shari’ar zaben gwamnan jihar Kano na 2023.
A rahoton da Daily Trust ta fitar a yammacin Litinin, ta tabbatar da cewa a ranar Alhamis dinnan za a fara sauraron shari’ar.
Abba Kabir Yusuf wanda bai gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ba, ya garzaya kotun koli domin ya iya rike kujerarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya je kotun koli
Kusan wata guda kenan da lauyan gwamnan, Wole Olanipekun SAN ya shigar da korafi a gaban babban kotun na Najeriya.
Lauyan ya tunkari kotun koli bayan an samu rudani a takardun CTC da aka fitar a kan hukuncin babban kotun da ke Abuja.
Kano: NNPP za ta tsira a kotun koli?
Wole Olanipekun SAN ya ce Alkalan kotun daukaka kara sun yi kuskure da su ka bari aka zaftarewa NNPP kuri’u 160, 000.
Babban lauyan ya ce kotun ba ta da hurumin sake dauko maganar zama 'dan jam’iyya wanda lauyoyin APC ba su gabatar ba.
Ko da an shigar da karar, Olanipekun ya fadawa kotu tayi watsi da batun domin babu ruwan kotu da sha'anin rajistar NNPP.
APC v NNPP a shari'ar zaben Gwamnan Kano
Ana sa ran yanzu Alkalin alkalai ya zabi alkalan da za su saurari wannan shari’a da za ta warware gardamar zaben jihar Kano.
Politics Digest ta ce kotun koli ta sanar da ranar zaman ga wadanda za ayi shari'ar da su.
"Ayi ta addu'a" - Masoyan Abba
Abba Kabir Yusuf wanda ya lashe zaben gwamna a 2023 ya samu kan shi a matsala da APC ta kai kara a kotun korafin zabe.
Magoya bayan Abba Gida Gida sun bukaci a cigaba da addu’a inda jam’iyyar APC kuma ta ce ba za ayi sulhu a wajen kotu ba.
Asali: Legit.ng