Abba, Caleb Da Gwamnonin Jihohi 13 Da Za A Yi Shari’ar Zaben 2023 Da Su a Kotun Koli
- A Kotun Koli za a san wanane zai mulki jihohin Bauchi, Legas, Nasarawa, Sokoto da Benuwai a matsayin gwamna
- Akwai jihohi fiye da 10 da yanzu ake shari’a da gwamnoninsu a kotun koli, Alkalai ba su kai ga yanke hukunci ba
- Shari’ar zaben Abba Kabir Yusuf da Caleb Muftwang a jihohin Kano da Filato sun fi daukar hankali a zaben 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Har yau ba a kammala shari’ar zaben gwamnonin 2023 a jihohi ba, yanzu haka akwai kararrakin da ke kotun kolin kasar.
Vanguard ta ce jam’iyyun adawa da masu mulki sun daukaka kara a Kano, Filato, Abia, Delta, Kuros Riba, Ribas, Legas da Sokoto.
Sauran jihohin sun hada da Nasarawa, Benuwai, Akwa Ibom, Taraba da kuma Bauchi.
1. Sokoto
Mallam Saidu Umar bai gamsu da hukuncin da Alkalai su ka yi a kan zaben 2023, yana kalubalantar nasarar Gwamna Ahmad Aliyu a kotun koli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Legas
Har yanzu jam’iyyar PDP ba ta hakura da kujerar gwamnan Legas ba duk da na uku ta zo a zaben da Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya samu galaba.
3. Nasarawa
Da farko David Ombugadu ya samu nasara a kotun zabe, sai daga baya aka tabbatar da nasarar Abdullahi Sule, yanzu an daukaka kara a Nasarawa.
4. Benuwai
‘Dan takaran PDP a zaben 2023, Titus Tyoapine Uba ya tafi kotun daukaka kara da nufin raba Hyacinth Alia daga kujerar gwamna jihar Benuwai.
5. Ribas
Da alama Beatrice Itubo da Tonye Cole za su kalubalanci zaben Simi Fubara a kotun koli bayan hukuncin kotun korafin zabe da na daukaka kara.
6. Filato
Caleb Muftwang ya rasa kujerarsa a kotun daukaka kara a watan jiya. Babban kotun za ta raba gardamarsa da Nentane Yiltada na jam’iyyar APC.
7. Akwa Ibom
Duk da galabar da Umo Eno ya samu a filin zabe da kotu, jaridar ta ce gwamnan jihar Akwa Ibom. YPP, APC da AA sun tafi gaban Alkalan kotun koli.
8. Kuros Ribas
Farfesa Sandy Onor ya taso Gwamna Bassey Out a gaba kuma har yau bai hakura ba. Bayan ya sha kashi, ya daukaka kara domin a tsige gwamnan.
9. Bauchi
Air Marshal Saddique Abubakar wanda ya yi wa APC takarar gwamnan Bauchi a 2023 ya dumfari kotun koli domin a sauke Bala Mohammed da PDP.
10. Taraba
A jihar Taraba, ‘dan takaran jam’iyyar NNPP a zaben gwamna, Farfesa Sani Yahaya ya je kotun yana ikirarin Gwamna Kefas Agbu bai lashe zabe ba.
11. Delta
Akalla jam’iyyu suna kalubalantar zaben Sheriff Oborevwori da PDP a Delta. Ovie Omo-Agege da Kenneth Gbagi na APC da SDP sun daukaka kara.
12. Kano
Abba Kabir Yusuf da NNPP sun rasa duka shari’o’in da aka yi na zaben Kano ga APC. Ana jiran kotun koli tayi hukuncin karshe a kan shari’ar gwamnan.
"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya
Abba Gida Gida da Nasiru Gawuna
Bayan an tsige shi a kotun sauraron korafin zabe, Abba Kabir Yusuf ya dauki hayan lauyan Bola Tinubu watau Wole Olanipekun ya daukaka kara.
Wole Olanipekun SAN ne ya tsayawa NNPP a babban kotun amma duk da haka ba a dace ba, daga nan ya shigar da karar karshe zuwa kotun koli.
Asali: Legit.ng