‘Yan APC Sun Fara Harin Matsayi Tun da Ministan Tinubu Ya Hango Kujerar Sanata

‘Yan APC Sun Fara Harin Matsayi Tun da Ministan Tinubu Ya Hango Kujerar Sanata

  • Kotu ta ayyana Ministan kwadago Simon Bako Lalong a matsayin zababben Sanatan kudancin jihar Filato a majalisar dattawa
  • Muddin tsohon gwamnan ya tafi majalisar tarayya, dole zai hakura da kujerar da yake kai ta Minista, sai a maye gurbinsa da wani
  • Yanayin siyasar Filato ya nuna Lalong zai iya hakura da FEC, matsalar ita ce a cikin APC wa za a dauko ya zama sabon Minista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jiga-jigan jam’iyyar APC da-dama sun fara neman yadda za su samu kujerar Minista idan har Simon Bako Lalong ya zabin yin murabus.

Wani dogon rahoto na Daily Trust ya nuna cewa akwai wadanda su ke neman kujerar Minista daga jihar Filato idan aka samu gurbi a FEC.

Kara karanta wannan

An kawo wata dabarar tsige Gwamnan PDP, Magoya bayan Minista ba su hakura ba

Simon Lalong
Simon Lalong zai iya barin Minista ya zama Sanata Hoto: @LalongBako
Asali: Twitter

Lalong: Minista a gwamnati ko Sanata a Majalisa?

Idan tsohon gwamnan na Filato ya zabi ya tafi majalisar dattawa, za a samu rabuwar kai tsakanin ‘ya ‘yan APC a kan wanda zai gaji kujerarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban karamar hukumar Kanam, Farfesa Saleh Mohammed Kanam yana cikin wadanda ake ganin sun fara kwalla rai a kan kujerar.

Wata majiyar jaridar ta ce Farfesan yana da goyon bayan Dr Nentawe Yilwatda wanda zai iya zama gwamna da su Honarabul Yusuf Gagdi.

Farfesohi na tseren Minista a gwamnatin APC

Wani Farfesan da ake tunani shi ne Dakas Dakas, wanda ya rike babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a a lokacin Simon Lalong.

Shi ma Farfesa Dakas zai dace da kujerar Minista saboda ilmin bokonsa. Sannan ‘dan APC ne da ake ta rade-radin zai samu mukami a gwamnati.

Kara karanta wannan

Shari'ar Kano: Lauya mazaunin Kano ya yi hasashen damar Abba Kabir a Kotun Koli

Leadership ta ce shugaban majalisar ARCN ta masu bincike a kan harkar gona, Farfesa Garba Sharubutu yana neman kujerar minstan tarayya.

Wasu suna ganin Lalong yana goyon bayan Farfesa Danladi Atu wanda ya yi masa SSG.

Idan Danladi Atu ya sha bam-bam da musamman Farfesa Kanam shi ne ana ganin bai da karfi sosai a siyasa, ya fi ido ne a wajen aikin gwamnati.

Wasu kuma su na kawo Komsol Alpanson wanda tsohon ‘dan majalisa ne da tsohon kwamishina, Festus Fuanter wanda ya shiga APC-NWC a baya.

Ba a bin mamaki ba ne a ji sunan Bashir Musan Sati ko Sani Mudi idan za a canza Lalong.

Jigon APC ya ce dole Tinubu ya yi gyara

An ji Salihu Lukman ya ce shaharar Bola Ahmed Tinubu a siyasa ta taimaka ya zama ‘dan takaran APC amma kuma bai gamsu da mulkinsa ba.

Watanni shida da hawa mulki, jagoran APC ya ce babu bambanci tsakanin mulkin sabon shugaban kasa Bola Tinubu da Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng