Shari’ar Kano: Lauya Mazaunin Kano Ya Yi Hasashen Damar Abba Kabir a Kotun Koli

Shari’ar Kano: Lauya Mazaunin Kano Ya Yi Hasashen Damar Abba Kabir a Kotun Koli

  • Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a shari’ar zaben Kano, wani lauya mazaunin Kano ya yi hasashen abin da zai faru
  • Lauyan mai suna Umar Sa’ad Hassan ya bayyana cewa zai yi matukar wahala Gwamna Abba Kabir ya yi nasara a kotun
  • Ya kara da cewa dukkan korafe-korafen da aka gudanar a kansa ya gagara kare kanshi tun daga zaftare kuri’u har cewa ba dan jam’iyya ba ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano Wani babban lauya da ke jihar Kano, Umar Sa’ad Hassan ya yi hasashen abin da zai faru a shari’ar zaben jihar Kano.

Hassan ya bayyana yadda Gwamna Abba Kabir zai iya rasa dama a hukuncin Kotun Koli da ake dako a jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano ya bayyana gaskiyar zaman Abba 'dan NNPP kafin hukuncin kotun koli

Lauyan Kano ya yi hasashen damar Abba Kabir a shari'ar zaben jihar
Shari’ar Kano: Lauya ya yi hasashen abin da zai kasance a shari'ar zaben jihar. Hoto: Abba Kabir, Nasiru Gawuna.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a baya?

Gwamnan ya daukaka kara ne bayan kotu ta sake rusa zabensa da aka gudanar a watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun, yayin hukuncinta, ta tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.

Da ya ke magana kan shari’ar yayin hira da Legit, Hassan ya ce zai yi wahala Abba Kabir ya samu nasara a Kotun Koli.

Ya ce jam’iyyar NNPP da Abba Kabir sun gaza kalubalantar tuhumarsu da ake yi a kan shari’ar.

Ya ce:

“A tunani na, zai yi wahala ganin yadda kotun zabe ta zaftare kuri’u dubu 165 a cikin kuri’unsa, kuna ganin yadda aluyoyi ke maganar cewa akwai kuskure a ciki.
“Saboda dokar zabe ta ce idan malamin zabe ya tabbatar da su to babu matsala, tun farko kowa sai zuba Turanci ya ke yi ba tare da kawo hujja da za su wargaza hukuncin Kotun Daukaka Karar ba, zai yi wahala Yusuf ya yi nasara.”

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta bayyana hukuncin da ya kamata Kotun Koli ta yanke a shari'ar jihar Kano

Ya kara da cewa APC ta gabatar rijistar NNPP amma babu sunan Gwamna Yusuf a ciki saboda haka zai yi wahala ya kalubalnci hukuncin Kotun Daukaka Kara.

Ya ce duk da cewa mutanen Kano sun zabi Yusuf Abba dole za su ji haushi idan har kotu ta kwace kujera daga hannunsa.

Kungiya ta yi martani kan shari’ar Kano

A wani labarin, Kungiyar Matasan Arewa ta bukaci a yi hukuncin adalci a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.

Kungiyar ta bukaci Kotun Koli da ta bai wa mutanen Kano abin da su ka zaba don gudun ta da hankula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel