Wata Sabuwa Yayin da Aka Zargi Tinubu da Haddasa Rikicin Siyasa a Kano
- A watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta jihar Kano ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)
- Kotun zaben ta ayyana Nasiru Gawuna, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben na watan Maris
- Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun zaben a watan Nuwamba, sai dai magoya bayan jam'iyya mai mulki a Kano sun daura laifin rikicin siyasar jihar kan Shugaba Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kano, jihar Kano - Gamayyar kungiyoyin Arewa a yankin kudu maso yamma ta zargi Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da haddasa rikicin siyasa a jihar Kano.
Kamar yadda jaridar The Guardian ta rahoto a ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba, kungiyar ta yi zargin cewa Shugaban kasa Tinubu ne ke da hannu a rikicin da ke faruwa a jihar Kano a kokarinsa na son zarcewa a 2027.
‘Gwamnatin Tinubu na da burin murkushe Arewa’ – Kungiya
Jaridar The Sun ta nakalto kungiyar tana cewa gwamnatin Tinubu na aiki don murkushe arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jaridar, gamayyar kungiyoyin Arewa sun taru a cibiyar al'adu da ke Mokola a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, domin bayyana kokensu.
A cewarsu, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, wanda kotun zabe da kotun daukaka kara suka tsige shine zabin al'umma.
Wakilin kungiyar, Shehu Idris ya bayyana a yayin zanga-zangar cewa:
"Ana kokarin yi wa mutane fashi da tsakar rana da karkatar da muradin su ta hanyar kutuna a jihar Kano. Ba lallai ne mutane su yarda da wannan ba.
“Akwai abin takaici, mutanenmu suna jin cewa wannan duk ya faru ne kudirin Shugaba Bola Tinubu na son zarcewa a wa’adi na biyu, wanda bai kai ga cinye wa’adinsa na farko ba. Kiyayyar Yarabawa na karuwa a Arewa saboda haka.”
Legit Hausa ta zanta da wani dan APC mai suna Malam Aliyu Yusuf don jin ta bakinsa inda ya ce lallai babu ruwan Tinubu a siyasar Kano dama dai jam’iyyarsu ce ta ci zabe.
Malam Yusuf ya ce:
“A zahirin gaskiya ba ruwan shugaban ƙasa a batun shari'ar Kano, idan ana gaban shari'a, su fa alkalai hujjojin da kowane ɓangare ya gabatar suke kallo su yanke hukunci.
“Dama can APC ta ci zabe amma suka yi amfani da wata dama suka yi aringizon kuri'u, gaskiya ce take ƙara bayyana kuma Gawuna dai ya zo, saura rantsarwa kawai muke jira, amma kotun koli ba abinda zata da ya wuce goyon bayan gaskiya kamar yadda kotuna biyu na baya suka yi.”
Gwamnan Kano ya yi alhinin rashin Asma'u
A wani labari na daban, mun ji cewa Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano, ya nuna bakin ciki matuka kan mutuwar Asma'u Sani, yarinyar da ke fama da cutar kansa a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba.
Legit Hausa ta samu labarin cewa Asma'u ta rasu ne a safiyar ranar Larba, 6 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng