Kungiyoyin Arewa Sun Faɗi Hukuncin da Ya Kamata Kotun Koli Ta Yanke Kan Zaben Gwamnoni 3

Kungiyoyin Arewa Sun Faɗi Hukuncin da Ya Kamata Kotun Koli Ta Yanke Kan Zaben Gwamnoni 3

  • Wasu kungiyoyin arewa sun bayyana hukuncin da ya kamata kotun koli ta yanke kan nasarar gwamnonin Kano, Zamfara da Filato
  • A cewar shugaban gamayyar ƙungiyoyin, ya kamata kotun koli ta tabbatar da zaɓin da talakawa suka yi a watan Maris
  • Sun nemi a soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, a maida wa Abba Kabir, Dauda Lawal da Celeb Mutfwang nasarar da suka samu a zaɓe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Har yanzun masana, yan siyasa masu sharhi da kungiyoyi na ci gaba da martani dangane da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na soke zaɓen gwamnonin Kano, Zamfara da Filato.

Kotun kolin Najeriya.
Wasu Kungiyoyin Arewa Sun Nemi Kotun Koli Ta Tabbatar da Zabin Mutane a Jihohi Uku
Asali: UGC

Wata ƙungiya mai suna, Northern Initiative for Peace and Economic Development, ta buƙaci kotun koli ta rushe hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnonin jihohin uku.

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya ƙara samun gagarumin goyon baya da ka iya sa ya lallasa Abba a Kotun Koli

A wata sanarwa ranar Laraba, ƙungiyar ta roki kotun koli ta jingine hukuncin kana ta tabbatar da nasarar waɗanda jama'a suka kaɗa wa kuri'unsu ranar zaɓe, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikin arewa tare da gamayyar wasu ƙungiyoyi sun nuna damuwarsu kan maida ƙasar ta ta jam'iyya ɗaya.

Jagoran kungiyoyin, Abel Jilemsam, ya ce zaman lafiyar jihohin Kano da Filato da Zamfara na da matukar muhimmanci ga Najeriya.

A cewarsa, zabukan gwamnonin da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023, a Kano, Filato da Zamfara sun nuna hadin kan al’umma wajen tsara makomar jihohinsu.

Wane hukunci ya dace kotun koli ta yanke?

Ya kuma ƙara da cewa abu mai muhimmanci shi ne a maida wa waɗanda talakawa suka zaɓa hakkinsu domin ƙara daraja tsarin demokuraɗiyya a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kano: Lauyoyin jihohi 19 sun ƙara gano wata matsala a hukuncin tsige Abba, sun bayyana mafita

A kalamansa, shugaban tawagar ƙungiyoyin ya ce:

“Al’ummar Kano, Filato da Zamfara sun yi amfani da ‘yancinsu na dimokuradiyya sun zabi waɗanda suka aminta da su, dole a saurari muryoyin su a mutunta su."
"Muna kira ga masu ruwa da tsaki da suka hada da hukumomin zabe da kuma bangaren shari’a da su tabbatar an yi hukunci ba tare da son zuciya ba a kotun koli."
“Domin yauƙaƙa hadin kai da ci gaba, muna kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su ba da fifiko ga al’umma da kuma mutunta sakamakon abin da mutane suka zaɓa."

PDP ta fara shirin magance matsalolinta

A wani rahoton kuma Babbar jam'iyyar adawa ta fara ɗaukar matakan magance matsalolin cikin gida da suka haɗa mambobinta faɗa.

A taron kwamitin gudanarwa (NWC) na ƙasa, PDP ta umarci 'ya'yanta su janye ƙararrakin da suka shigar a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262