Taurin bashi ya jawo AMCON tana tattare wasu dukiyoyin Jimoh Ibrahim

Taurin bashi ya jawo AMCON tana tattare wasu dukiyoyin Jimoh Ibrahim

- Gwamnatin Tarayya ta fara raba Jimoh Ibrahim da wasu kadarorinsa

- An dauki wannan matakin ne bayan ‘dan kasuwar ya gaza biyan bashi

- AMCON ta ce ana bin Jimoh Ibrahim bashi na kusan Naira biliyan 70

Hukumar AMCON mai alhakin kula da kadarorin Najeriya, ta ce ta karbe wasu dukiyoyi da ‘dan kasuwar nan, Jimoh Ibrahim ya mallaka.

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, gwamnati ta karbe kadarorin gawurtaccen attajirin ne saboda tarin bashin da ke kansa.

Rahotanni sun bayyana cewa bashin da ke kan Mista Jimoh Ibrahim ya haura Naira biliyan 69.4.

KU KARANTA: Mutumin Yobe ya ci kyautar kudi N150m a wajen gasar kimiyya

A halin yanzu ana rufe duk wasu asusun banki da ke dauke da sunan Jimoh Ibrahim da kamfanoninsa; Global Fleet Oil & Gas Limited.

Hukumar AMCON ta ce ba ta kyale kamfanin ‘dan kasuwar na NICON Investment Limited ba.

Pinheiro Legal Partners a madadin AMCON ya yi nasarar karbe kamfanin NICON Investment da ake da su a garuruwan Legas, Abuja da Fatakwal.

Bayan haka an rufe ofisoshin kamfanin International Hotels Limited da ke Legas da wani ginin tsohon bankin Allied Bank duk a garin na Legas.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun lafta N100m a kan ‘Yan Sandan da aka sace

Taurin bashi ya jawo AMCON tana tattare wasu dukiyoyin Jimoh Ibrahim
Jimoh Ibrahim Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Jaridar ta ce an rufe katafaren otel dinnan na NICON a Maitama da Garki a birnin tarayya Abuja.

Alkali R.M Aikawa na babban kotun tarayya a Legas ne ya hallata wa AMCON karbe kadarorin ‘dan kasuwar da aka san da su saboda kin biyan bashi.

Mai magana da yawun bakin AMCON, Jude Nwauzor, ya ce sun yi nasarar raba ‘dan kasuwar da dukiyoyinsa, bayan sun samu hadin-kan ‘yan sanda.

Dazu kun ji Gwamnan Akwa-Ibom ya karyata rahoton da ke yawo na cewa ya yi facaka da biliyoyan 10 wajen sayen motoci, mai da yi wa baki masauki.

Ana zargin Gwamnan na PDP da tafka mahaukaciyar badakala, amma ya musanya maganar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel