Wasu Jiga-Jigan NNPP Sun Kara Jefa Gwamna Abba da Kwankwaso Cikin Babbar Matsala, Gaskiya Ta Bayyana

Wasu Jiga-Jigan NNPP Sun Kara Jefa Gwamna Abba da Kwankwaso Cikin Babbar Matsala, Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu korarrun mambobin NNPP na neman sake jawo wa Gwamna Abba Kabur Yusuf da Kwankwaso matsala
  • Sun fito suna yaɗa cewa Abba ba ɗan NNPP bane kuma an kori Kwankwaso, amma jam'iyyar ta fito ta bayyana gaskiya
  • Mamban kwamitin gudanarwa (NWC), Ladipo Johnson, ya ce ikirarin da tsoffin jiga-jigan NNPP suka yi ba gaskiya bane

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ce wasu korarrun ‘ya’yan jam’iyyar na kokarin yada labaran karya kan Gwamna Abba Yusuf na Kano da Rabiu Kwankwaso.

Gwamna Abba Tare da Kwankwaso.
Korarrun Mambobi Na Kokarin Bata Sunan Abba da Kwankwaso, NNPP Ta Magantu Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mamban kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), Ladipo Johnson, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar Labour Party ta caccaki Peter Obi, bayanai sun fito

Ya yi zargin cewa wasu korarrun mambobin NNPP ƙarƙashin jagorancin Tope Aluko sun fara yaɗa ƙaryar cewa Gwamna Abba ba ɗan jam'iyya bane lokacin da ya tsaya takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma Mista Jonson ya ce tawagar korarrun suna yaɗa cewa NNPP ta kori Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Menene gaskiyar wannan magana?

Amma Mista Jonson ya bayyana cewa dukkan waɗanda bayanan da suke yaɗawa, "karya ce mara tushe balle makama."

A kalamansa ya ce:

"Mun samu rahoton cewa wasu tsirarun korarrun mambobin NNPP ciki harda Tope Aluko da wasu tsoffin shugabannin jihohi sun kira taron yan jarida a Abuja suna yaɗa farfaganda."
"Suna yaɗa cewa mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ba ɗan NNPP bane lokacin da ya tsaya takara da kuma cewa an kori Sanata Rabiu Kwankwaso daga jam'iyya."

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya ƙara samun gagarumin goyon baya da ka iya sa ya lallasa Abba a Kotun Koli

"Wannan karya ce mara tushe, muna da tabbacin Abba Gida-Gida cikakken ɗan NNPP ne a lokacin zaɓe kuma mun yi imani kotun kolin Najeriya zata yi adalci."

Daga ƙarshe, Jonson ya yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su kauracewa kalaman waɗannan mutanen da ba su ƙaunarsu.

"Muna tunatar da jama’a cewa Cif Boniface Aniebonam daya daga cikin wadanda suka kafa NNPP ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ya nemi a tabbatar masa da nasarar da ya samu," in ji shi.

Majalisa Ta Dakatar 'Yan Majalisa Huɗu a Benue

A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Benuwai ta dakatar da mambobi guda huɗu kan faɗa da yan majalisa masu goyon bayan Gwamna Alia.

Wannan matakin ne zuwa ne yayin da rikicin cikin gida ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262