Rigima Ta Ɓarke a APC, Majalisa Ta Dakatar 'Yan Majalisa Huɗu kan Muhimmin Abu 1

Rigima Ta Ɓarke a APC, Majalisa Ta Dakatar 'Yan Majalisa Huɗu kan Muhimmin Abu 1

  • Majalisar dokokin jihar Benuwai ta dakatar da mambobi guda huɗu kan faɗa da yan majalisa masu goyon bayan Gwamna Alia
  • Wannan matakin ne zuwa ne yayin da rikicin cikin gida ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar
  • Shugabannin APC da Gwamna Alia sun fara takun saƙa ne kan tsarin da ya zo da shi na raba mukaman gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Rigingimun cikin gida da ke faruwa a jam'iyyar APC reshen jihar Benuwai ya fara jawo mata matsala a ranar Litinin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Majalisar dokokin jihar Benue.
Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar da Yan Majalisa Hudu Daga Aiki Hoto: Benue State House Of Assembly

Majalisar dokokin jihar ta dakatar da ƴan majalisa hudu daga aiki biyo bayan kace-nace da ya haɗa su da wasu mambobin majalisa masu goyon bayan Gwamna Hyacinth Alia.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa mutane 7 a manyan muƙaman hukumar NIS ta kasa, sunaye sun bayyana

An tattaro cewa majalisar ta dakatar da yan majalisun ne bisa zargin yin zagon ƙasa ga zaman majalisar dokoki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan majalisa hudu da aka dakatar

Waɗanda majalisar ta dakatar sun haɗa da Solomon Gyila, mamba mai wakiltar mazaɓar Gwer ta yamma da Douglass Akya, mamba mai wakiltar mazaɓar Makurdi ta kudu.

Sauran su ne, Dyako Ashwa, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Konshisha da kuma na karshe, Anthony Agom, mai wakiltar mazaɓar Okpokwu a majalisar jihar Benuwai.

Rikicin da ya ɓarke a APC

Wannan dakatarwa na zuwa ne bayan dattawan APC a jihar sun yi taro a gidan gwamnati da ke Makurɗi domin kaɗa kuri'ar ƙwarin guiwa kan Gwamna Alia.

Sun yi haka ne duk da shugabannin jam'iyya na matakin jiha da ƙananan hukumomi sun fara juya wa gwamnan baya.

Dattawan APC karkashin tsohon shugaban majalisar dattawa, Ameh Ebute, da wasu da dama sun kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin warware duk wasu matsalolin cikin gida.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya buƙaci mataimakin gwamnan APC ya sa hannu a takardar murabus kan abu 1 tal

Tun a watan Yunin 2023 ne dai shugabannin jam'iyyar APC na jihar Benue da gwamnan ke takun-saka kan tsarin raba muƙamai, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kungiyar Lauyoyi Ta Soki Hukuncin Tsige Abba Kabir Yusuf

A wani rahoton kuma Kungiyar matasan lauyoyin jihohin arewa 19 sun caccaki hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa hukuncin ya nuna rashin adalci ƙarara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262