Masu Ruwa da Tsakin NNPP Na Arewa Maso Gabas Sun Taso Kwankwaso a Gaba

Masu Ruwa da Tsakin NNPP Na Arewa Maso Gabas Sun Taso Kwankwaso a Gaba

  • Shugabannin NNPP na shiyyar Arewa maso Gabas sun juyawa Rabiu Kwankwaso baya, sun ce suna goyon bayan korar da aka masa
  • Mambobin majalisar zartarwa da masu ruwa da tsaki na NNPP a shiyyar sun zargi Kwankwaso da hannu a rikocin cikin gida da ke faruwa
  • Sun kuma jaddada goyon bayansu ga Gwamna Abba wanda kotun ɗaukaka ƙara ta tsige, sun nemi a sa shi a addu'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwamitin zartarwa da masu ruwa da tsaki na New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen Arewa maso Gabas sun jaddada matsayar korar Rabiu Kwankwaso daga jam'iyyar NNPP.

Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir.
Masu Ruwa da Tsakin NNPP Na Arewa Maso Gabas Sun Taso Kwankwaso a Gaba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Sun zargi Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 karkashin inuwar NNPP, da hannu a haddasa rigingimun cikin gida a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya buƙaci mataimakin gwamnan APC ya sa hannu a takardar murabus kan abu 1 tal

Kusoshin jam'iyyar NNPP sun cimma wannan matsaya ne a taron majalisar zartarwa da masu ruwa da tsaki na Arewa maso Gabas, wanda ya gudana a Bauchi ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Leadership ya ce a wata sanarwa da suka fitar bayan ƙarkare taron, masu ruwa da tsakin sun ɗora alhakin rashin nasarar NNPP da rikicin da take ciki kan Kwankwaso.

Sun maida martani kan tsige Gwamna Abba na Kano

Bugu da ƙari, shugabannin NNPP na shiyyar Arewa maso Gabas sun nuna takaicinsu kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.

Da yake jawabi a madadin sauran, mataimakin shugaban NNPP na Arewa, Dakta Babayo Liman, ya sha alwashin cewa za su ci gaba da goyon bayan Abba Gida-Gida.

Ya kuma roƙi ɗaukacin mambobin jam'iyyar da magoya baya a faɗin ƙasar nan su ci gaba marawa gwamnatin Kano baya tare sanya Abba a cikin addu'o'insu.

Kara karanta wannan

Dubun wasu hatsabiban 'yan bindiga 8 da suka addabi mutane ya cika a jihar Kaduna

Daga ƙarshe mahalarta taron sun jaddada matsayar da aka cimma na rusa kwamitin gudanarwa na kasa karkashin jagorancin Abba Kawu Ali, Vanguard ta ruwaito.

Yadda Tinubu ya sasanta rikicin siyasar jihar Ondo

A wani rahoton na daban Shugaba Tinubu, ya nemi mataimakin gwamnann Ondo ya sa hannu kan takardar murabus kuma ya kai masa.

Wannan na ɗaya daga cikin matakan da aka aminta da su a wurin taron sulhunta rikicin siyasar jihar Ondo, a cewar kwamishinar yaɗa labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel