Mataimakin Gwamnan PDP Ya Daga Wa Mai Gidansa Yatsa, Ya Fito Takarar Gwamna a Jihar

Mataimakin Gwamnan PDP Ya Daga Wa Mai Gidansa Yatsa, Ya Fito Takarar Gwamna a Jihar

  • A karshe, Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo ya bayyana kudurinsa na neman takarar gwamna a jihar
  • Shaibu ya bayyana kudirin nasa ne a yau Litinin 27 ga watan Nuwamba a birnin Benin City a cibiyar Biohop Kelly
  • Wannan na zuwa ne yayin da Shaibu ke ci gaba da zaman doya da manja da mai gidansa, Gwamna Godwin Obaseki na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya fito neman takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP.

Shaibu ya fito takarar ce a jam'iyyar PDP mai mulki wanda Gwamna Godwin Obaseki ke jagoranta, cewar Daily Trust.

Mataimakin gwamna ya bayyana kudirinsa na tsaya wa takara a zabe
Philip Shaibu ya ayyana neman takarar gwamna a jihar Edo. Hoto: Godwin Obaseki, Philip Shaibu.
Asali: Facebook

Yaushe Shaibu ya bayyana kudirinsa?

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ɗau zafi, ya dakatar da kwamishina da wani babban hadimi kan abu 1 tak

Mataimakin gwamnan ya bayyana kudirin nasa ne a yau Litinin 27 ga watan Nuwamba a Cibiyar Biohop Kelly da ke birnin Benin City a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a matsayinsa na wanda ya san ciki da wajen jihar, ya yi alkawarin inganta rayuwar al'ummar jihar.

Ya sha alwashin cewa babu mai dakatar da shi a zaben da za a gudanar a shekarar 2024 da za a gudanar a jihar.

Shaibu ya ce ya yi aiki da Gwamna Obaseki na tsawon shekaru bakwai wanda hakan ya ba shi damar gina tubalin inganta jihar.

Wane roko Shaibu ya yi wa 'yan jihar?

Dan takarar ya roki 'yan jihar da su ba shi dama don cimma burinsa na zama gwamnan jihar, Channels TV ta tattaro.

Tun farko, Shaibu ya so kaddamar da kudurinsa a otal na Eterno amma otal din sun sauya tunani inda su ka ce Gwamna Obaseki ya na da taro a wurin.

Kara karanta wannan

Bayan shari'ar Nasarawa, kotu ta sake yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC, ta ba da dalili

Gwamnan da mataimakinsa su na ci gaba da samun matsala tun bayan sanar da kudurinsa na neman takarar gwamna a jihar.

Shaibu ya kwashe kayansa a gidan gwamnati

A wani labarin, mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya kwace kayansa daga gidan gwamnatin jihar zuwa sabon ofishinsa.

Wannan na zuwa yayin da Shaibu ke ci gaba da samun matsala tsakaninsa da mai gidansa, Gwamna Godwin Obaseki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel