Wani Bafullatani Ya Datse Hannun Abokinsa Kan Lemun Kwalba a Jihar Ogun

Wani Bafullatani Ya Datse Hannun Abokinsa Kan Lemun Kwalba a Jihar Ogun

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun sun ce sun fara gudanar da bincike kan wani fada da ya kaure tsakanin wasu abokai biyu daga rugar fulani ta Ogunmakin
  • Rikicin ya faru ne sakamakon sabanin da abokan suka samu kan lemun kwalba, lamarin da ya ja aka datse hannun daya, yayin da aka huda cikin dayan
  • Wannan mummunan lamari da ya faru, ya jefa al'ummar fulanin cikin radani da firgici, kasancewar kowanne daga cikin abokan na iya rasa rayuwarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ogun - Al’ummar Fulani mazauna yankin Ogunmakin a jihar Ogun sun shiga cikin rudani da a ranar Litinin da ta gabata, yayin da wasu abokai guda biyu, Abdullahi Audu da Usman Muhammed suka kusa kashe junansu sakamakon sabani da suka samu kanlemun kwalba.

Kara karanta wannan

Mutane 37 sun mutu wurin neman shiga aikin soja a kasar Congo

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Audu wanda aka ce shi ne ya fara wannan rikicin, ya zaro adda tare da datse hannun Muhammad a lokacin fadan.

Rundunar 'yan sandan Najeriya
Rikicin da ya barke ya bar abokan rai a hannun Allah bayan datse hannun daya, da huda cikin dayan Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

Rikicin ya yi muni bayan 'yan hanjin daya sun fito waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin an datse hannunsa gaba daya, shi ma Muhammed ya zaro wuka ya soke cikin Audu, abin da ake kyautata zaton ramuwar gayya ce kafin mutane su shiga tsakanin su.

Sai dai lamarin ya kara yin muni a lokacin da wukar da Muhammed ya soka wa Audu a ciki ta fito da 'yan hanjin Audu, lamarin da ya kwantar da su gaba daya rai a hannun Allah.

Ganin rikicin da ya barke tsakanin abokanan biyu, sarkin fulanin yankin, Alhaji Wakili, ya garzaya ofishin ‘yan sanda na Owode Egba domin kai rahoton faruwar lamarin.

Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan lamarin

Kara karanta wannan

Bayan sauka mulki, Muhammadu Buhari ya faɗi manufa 1 tal da ta sa ya canza takardun naira a Najeriya

Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa a halin yanzu dukkan wadanda abin ya shafa suna karbar magani a wani asibitin da ke garin.

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Omolola Odutola, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce sun fara gudanar da bincike.

“Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, muna kan bincike,” Odutola ta bayyana hakan a wani sakon WhatsApp a ranar Talata.

Mutane 37 sun mutu wurin neman shiga aikin soja a kasar Congo

A wani labarin, akalla matasa 37 ne rahotanni suka bayyana sun mutu sakamakon wani turmutsutsu da ya barke a filin wasa na Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Congo.

Matasan sun je filin ne domin a tantance su a wani shiri da hukumar sojin kasar ke yi na daukar matasa 1,500 aiki, lamarin da ya jikkata mutane da dama, jaridar Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel