Daga Adamawa Zuwa Zamfara: Jerin Jihohin Da APC, PDP da Sauransu Suka Lashe a Zaben 2023

Daga Adamawa Zuwa Zamfara: Jerin Jihohin Da APC, PDP da Sauransu Suka Lashe a Zaben 2023

Bayan gudanar da zaben gwamnoni na 2023 a fadin jihohi 28 da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi a ranakun 18 ga watan Maris da 15 ga watan Afrilu, Legit.ng ta duba sakamakon, tare da zakulo rawar ganin da manyan jam’iyyu suka taka.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka samu dawowa a karo na biyu
Daga Kano Zuwa Yobe: Jerin Jihohin Da APC, NNPP, PDP Suka Lashe Zuwa Yanzu a Zaben Gwamnonin 2023 Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Wannan rahoton ya lissafo jerin jihohin da jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da sauransu suka lashe da kuma wanda ya kubce masu.

Sabbin jihohin da PDP ta kwato daga hannun APC

 1. Jihar Zamfara (Dauda Lawal)
 2. Jihar Plateau (Caleb Mutfwang)

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sabuwar jihar da APC ta kwace daga hannun PDP

 1. Jihar Benue (Rev Fr Hyacinth Alia)

Sabuwar jihar da NNPP ta kwace daga hannun APC

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Jam'iyyar APC Ta Kori Babban Sanata Mai Ci a Jihar Arewa, Ta Bayar Da Dalilai

 1. Jihar Kano (Abba Kabir Yusuf)

Sabuwar jihar da NNPP ta kwace daga hannun PDP

 1. Jihar Abia (Alex Otti)

Jihohin da APC ke ci gaba da iko a cikinsu

 1. Jihar Yobe (Gwamna Mai Mala Buni)
 2. Jihar Ogun (Gwamna Dapo Abiodun)
 3. Jihar Gombe (Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya)
 4. Jihar Jigawa (Umar Namadi)
 5. Jihar Kwara (Gwamna AbdulRazaq AbdulRahman)
 6. Jihar Lagos (Gwamna Babajide Sanwo-Olu)
 7. Jihar Sokoto (Aliyu Ahmed)
 8. Jihar Nasarawa (Gwamna Abdullahi Sule)
 9. Jihar Katsina (Dikko Rada)
 10. Jihar Kaduna (Uba Sani)
 11. Jihar Borno (Babagana Zulum)
 12. Jihar Ebonyi (Francis Nwifuru)
 13. Jihar Cross River (Bassey Otu)
 14. Jihar Niger (Umar Bago)
 15. Jihar Kebbi (Nasiru Idris)

Jihohin da PDP ke ci gaba da iko a cikinsu

 1. Jihar Akwa Ibom (Umo Eno)
 2. Jihar Oyo (Seyi Makinde)
 3. Jihar Bauchi (Bala Mohammed)
 4. Jihar Rivers (Sim Fubara)
 5. Jihar Taraba (Kefas Agbu)
 6. Jihar Delta (Sheriff Oborevwori)
 7. Jihar Adamawa (Ahmadu Fintiri)
 8. Jihar Enugu (Peter Mbah)

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen 'Yan Takarar Gwamnan APC a Jihohi 3 da Suka Shiga Hannun INEC

Jihohin da ba a yi zaben gwamnonin 2023 a ciki ba

 1. Jihar Osun, PDP
 2. Jihar Ekiti, APC
 3. Jihar Edo, PDP
 4. Jihar Kogi, APC
 5. Jihar Ondo, APC
 6. Jihar Bayelsa, PDP
 7. Jihar Anambra, APGA
 8. Jihar Imo - APC

Wasu mutane sun ci zarafin kwamishinan zabe a Adamawa

A wani labarin, mun ji cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun ci mutuncin wani kwamishinan zabe na kasa a jihar Adamawa yayin zaben gwamnan 2023.

Mutanen dai sun tasa mutumin a gaba da wasu tambayoyi bayan sun tube masa tufafinsa gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel