Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

  • Shehu Sani ya yi Allah-wadai saboda Alkalan kotun daukaka kara sun yanke hukunci a ba APC kujerar gwamna a Filato
  • Fitaccen ‘dan siyasar yana da ra’ayin cewa fashi aka yi wa jam’iyyarsu ta PDP a shari’ar zaben gwamnan jihar Filaton 2023
  • Sanata Sani ya ba jam’iyyu shawarar su rika maida hankali sosai game da zaben shugabanni da shaidar rajistar ‘ya ‘yanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Shehu Sani wanda ya shahara a siyasar Najeriya, yana cikin wadanda suka soki hukuncin Kotun Daukaka Kara kan zaben Filato.

Tsohon sanatan ya yi magana a shafin Twitter kamar yadda ya saba tofa albarkacin baki a kan al’amuran yau da kullum a gida da waje.

Caleb Mutfwang
Shehu Sani ya soki kotu kan tsige Gwamnan Filato Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Alkalai sun sauke gwamnan Filato

Sanata Shehu Sani yana ganin ba daidai ba ne kotu ta tsige Gwamna Caleb Mutfwang, ta ba Dr. Nentawe Goshwe da APC nasara.

Kara karanta wannan

Danyen zanga-zanga ya biyo bayan tunbuke Gwamnan PDP da Kotu tayi a Jihar Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalai uku da suka zauna a Abuja sun soke galabar Mytfwanga wanda ya samu kuri’u 525,299 a PDP a zaben gwamna da aka gudanar.

Kotu ta ce INEC ta bada satifiket ga ‘dan takaran APC Goshwe wanda ya zo na biyu da kuri’u 481,370 saboda PDP ta sabawa umarnin kotu.

Maganar Shehu Sani kan tsige Gwamnan Filato

"Hukuncin kotun daukaka kara a kan nasarar gwamnan jihar Filato abin takaici ne, abin ki kuma abin ayi tir da shi.
Fashi aka tafka da rana tsaka a kan zabin al’umma. Alkalan kotu su na zama makarar birne damukaradiyya."

- Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya ce an kawo sabon salo

Da yake magana kafin nan, Sani wanda ya yi shekaru hudu a majalisar dattawa ya ce wajibi ne jam’iyyun siyasa su tashi tsaye a yanzu.

Kara karanta wannan

Wasu sun tsinke da lamarin Tinubu da Kotu ta tsige gwamnonin adawa 3 a kwana 4

"Yanzu da kotu ta ke amfani da rajistar jam’iyya, zaben shugabanni da tsaida ‘yan takara wajen rusa manyan zabuka, dole jam’iyyu su yi hattara da wadannan tarko.
Ku rika biyan kudin zama ‘yan jam’iyya duk wata kafin Alkalai su fara cewa a kawo masu takardar biyan kudin rajistar ‘ya ‘yan jam’iyya.

- Shehu Sani

PDP: Ana zanga-zanga a jihar Filato

Labari ya iso mana cewa a wasu garuruwan Filato, mazauna da magoya bayan PDP sun ji haushin tsige Gwamna Caleb Mutfwang da aka yi.

Tun jiya aka fara zanga-zanga a kananan hukumomin Filato saboda kotun daukaka kara ta sauke Gwamna bayan watanni kusan shida a ofis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel