‘Yan Najeriya Su Na da Wuyar Sha’ani’ Buhari Ya Bayyana Abu 1 da Jawo Matsala a Gwamnatinsa

‘Yan Najeriya Su Na da Wuyar Sha’ani’ Buhari Ya Bayyana Abu 1 da Jawo Matsala a Gwamnatinsa

  • Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa ya bayyana irin gwagwarmayar da ya yi na tabbatar da kawo sauyi a kasar
  • Buhari ya ce babu kasar da take da wuyar sha’ani a mulki irin Najeriya inda ya ce kowa gani ya ke shi ya kamata ya yi mulki
  • Ya bayyana jita-jitar masu gudanar da gwamnatinsa da ake kira ‘Cabal’ da cewa zai iya yiyuwa amma dai babu wanda ya karya doka ya sha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi duk abin da zai yi don ganin ya gyara kasar yayin mulkinsa.

Buhari ya ce sai dai ya bai wa mutane dama su yi alkalanci da kansu kan irin abubuwan da ya kawo na ci gaba a kasar, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Buhari ya ambaci babban rauni 1 da yake da shi wanda ya iya kawo cikas a mulkinsa

Buhari ya ce 'yan Najeriya su na da wuyar sha'ani wurin mulki, ya ce su ne alkalai
Buhari ya yi martani kan yadda wahalar mulkin 'yan Najeriya ya ke. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Mene Buhari ke cewa?

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na NTA wanda shi ne hirarsa ta farko bayan kammala wa’adinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ‘yan Najeriya na da wahalar sha’ani wurin mulkarsu saboda a kullum tunaninsu shi ne su ne ya kamata ke kan mulki ba wani ba, This Day ta tattaro.

Ya ce:

“Allah ya ba ni damar mulkar kasar nan, na yi iya kokari na kuma mutane ne ya kamata su yi alkalanci."

Wane shaida Buhari ya yi wa 'yan Najeriya?

Ya kara da cewa:

“Yan Najeriya sun fi kowa wahalar sha’ani, mutane sun san ‘yancinsu, su na tunanin su ya kamata su ke mulki ba kai ba.
“Su na kula da dukkan motsinka, dole ka yi ta kokari dare da rana don tabbatar da cewa ka kawo sauyi a kasar da kuma nuna kwarewa.”

Kara karanta wannan

“Da na koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari ya magantu kan zaryar da wasu ke yi a gidansa na Daura

Buhari ya ce ana ta jita-jitar cewa akwai masu gudanar da gwamnatinsa inda ya ce zai iya yiyuwa akwai amma sai dai babu wanda ya karya doka ya sha a mulkinsa.

Buhari ya yi martani kan mulkinsa a Najeriya

A wani labarin, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu abin da ya rasa bayan kammala mulkinsa a Najeria.

Buhari ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na NTA wanda shi ne karon farko bayan kammala mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.