An Sabunta: Cikakken Jerin Gwamnonin Da Kotu Ta Kwace Kujerunsu Kawo Yanzu

An Sabunta: Cikakken Jerin Gwamnonin Da Kotu Ta Kwace Kujerunsu Kawo Yanzu

Zaben shekarar 2023 na daya daga manyan zabe da aka gudanar a kasar wanda ya zo da abubuwan bazata da yawa musamman hukunce-hukuncen kotuna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Duk da korafe-korafen jama’a kan hukumar zabe ta INEC da kuma bangaren shari’a, zaben bai kasance iya tsakanin APC da PDP ba kadai.

Cikakken sunayen gwamnonin da aka kwace mulkinsu a kotu
Jerin Gwamnonin da Kotu Ta Kwace Kujerarsu a Najeriya. Hoto: Dauda Lawal, A. Sule, Abba Kabir.
Asali: Twitter

Jam’iyyun da ba a yi tsammani ba kamar LP da NNPP sun taka rawar gani inda su ka samu kujerun gwamnoni da ‘yan Majalisun Tarayya da na jihohi.

Wannan nasara bai wuce kokarin da hukumar zabe ta INEC ta yi ba duk da korafin jama’a a kanta na ba da dama ga ko wace jam’iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kotu ta tsige gwamnan Filato, alkalai sun ce APC ta ci zaben 2023

Legit ta jero muku gwamnonin da bayan cin zabe aka kwace kujerunsu a kotu:

1. Abba Gida Gida

Abba Kabir na daga cikin gwamnonin da su ka ci zabe a jam’iyyar NNPP amma ya rasa kujerar a kotun zabe da ta yi hukunci a watan Satumba.

Kotun bayan rusa zaben ta kuma tabbatar da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe.

Har ila yau, kotun daukaka kara ta sanya yau Juma’a a matsayin ranar yanke hukuncin shari’ar da ke da muhimmanci ga dukkan jam’iyyu.

2. Dauda Lawal Dare

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rasa kujerarshi bayan kotun daukaka kara ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Dauda ya yi takara a jam’iyyar PDP inda ya yi nasara kan Bello Matawalle na jam’iyyar APC wanda yanzu ya ke rike da mukamin Minista.

Kotun ta ba da umarnin sake zabe a wasu kananan hukumomi guda uku a jihar saboda kura-kurai da aka tafka.

Kara karanta wannan

Shari'ar Gwamnan Kano: NNPP ta bayyana matsayarta kan hukuncin Kotun Koli tare da matakin na gaba

3. Abdullahi Sule

Kotun zabe zabe har ila yau, ta kwace kujerar Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa wanda kuma dan jam’iyyar APC ne.

Kotun ta kuma tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar PDP, David Umbugadu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gwamna Sule ya daukaka kara wanda ake sa ran zai san makomarsa kafin karshen wannan wata da muke ciki ta Nuwamba.

4. Alex Otti

Gwamna Alex Otti shi ne gwamnan farko da aka fara tsigewa yayin hukuncin kotun zabe da ke zamanta a Kano, cewar Vanguard.

Otti wanda dan jam’iyyar LP ne ya daukaka kara wanda daga bisani ya samu nasara kan abokin hamayyarsa a watan Oktoba.

5. Caleb Mutfwang

Kotun da ke zamanta a Abuja ta kwace kujerar Caleb Miftwang, gwamnan jihar Plateau a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

Kazalika, kotun ta kuma ayyana Nentawe Goshwe a matsayin ainihin wanda ya lashe zaben ta kuma umurci Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya (INEC) ta mika takardan shaidan cin zabe ga dan takarar na APC.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

Yau za a yanke hukuncin shari’ar Kano

Kun ji cewa, a yau Juma’a 17 ga watan Nuwamba za a yanke hukuncin shari’ar zaben Kano.

Gwamnati ta tsaurara tsaro a fadin jihar don dakile duk wani rikici da ka iya biyo baya yayin hukuncin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel