2027: Atiku Ya Fara Kiran Obi, Kwankwaso da Sauran Jam’iyyun Adawa Su Hada Kai

2027: Atiku Ya Fara Kiran Obi, Kwankwaso da Sauran Jam’iyyun Adawa Su Hada Kai

  • Atiku Abubakar ya gamsu cewa idan har jam’iyyun hamayya ba su hada-kai ba, zai yi wahala a iya tsaida APC
  • Jagoran hamayyan Najeriyan ya zauna da shugabannin IPAC, ya nuna dole ne jam’iyyun adawa su dunkule tare
  • Idan aka samu hadin-kan sauran ‘yan adawa, Atiku yana ganin zaa kawo karshen kama-karyar da ya ce ana yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Atiku Abubakar wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya yi kira ga ‘yan adawa su hada kansu.

The Cable ta ce Alhaji Atiku Abubakar ya yi wannan kira ne a wani jawabi da ya fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Mista Paul Ibe.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun adawa sun cigaba da shirin hada kai domin yakar Tinubu da APC a 2027

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar da shugabannin IPAC Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

IPAC ta ziyarci Atiku Abubakar

A yayin da ya gana da shugabannin majalisar IPAC, ‘Dan takaran shugaban Najeriyan ya ce a halin yanzu ana neman murkushe hamayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Watanni bayan nasarar APC a kotun koli, Hadimin na ya ce Atiku Abubakar ya ja-kunne cewa jam’iyya mai-ci na neman kashe adawa.

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya yake cewa kare daraja da kimar damukaradiyya bai aikin wani mutum daya ba ne.

Kun zo nan a yau domin ku fada mana cewa ya kamata mu hada-kai domin mu tallata damukaradiyya.

"Amma gaskiyar lamarin shi ne damukaradiyyarmu tana neman komawa ‘yar jam’iyya guda; kuma idan aka samu irin haka, a manta da maganar damukaradiyya kawai."

- Atiku Abubakar

Atiku zai so 'yan adawa su hade?

Premium Times ta ce Atiku ya yi kira ga IPAC a karkashin jagorancin Yabagi Sani, ta hada-kan ‘yan adawa domin a yaki jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da za su rungumi jam'iyyar APC

Idan aka dunkule a inuwa guda, Atiku ya na ganin za a hana APC murkushe ‘yan adawa, abin da yake zargin an kama hanyar yi a Najeriya.

‘Dan siyasar ya zargi APC da yin mulkin kama-karya, ya ce dole a hada-kai domin a taka mata burki, ko kuwa yara da jikoki su koka nan gaba.

Ibe ya kara da cewa Atiku ya yi Allah-wadai da INEC, ya ce ta shirya mafi munin zabe a tarihi.

APC za ta karbe Kano da Filato?

Idan aka koma Arewa, an ji labari Gwamnonin Jihohin Kano, Nasarawa, Filato suna fuskantar barazanar shari’a bayan sun lashe zaben bana.

‘Yan Kwankwasiyya sun samu kwarin gwiwa da su ka dawo da duka kujerun ‘Yan majalisar tarayyansu a kotu, haka zalika mutanen APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng