Gombe 2019: Kungiyar IPAC ta fadawa Jama’a su bi bayan Jam’iyyar APC
- Kananan Jam'iyyu akalla 45 sun marawa APC baya a zaben Gwamnan Gombe
- IPAC tace Inuwa Yahaya na APC ne ya fi cancanta cikin masu neman mulkin
- Wadannan ‘Yan siyasa sun fadawa Mabiyan su da su zabi APC a zaben na bana
Kamar yadda mu ke samun labari, yayin da ake shirin zaben sabon gwamnan jihar Gombe, jam’iyyu 45 ne aka ji sun marawa Alhaji Inuwa Yahaya na jam’iyyar APC mai adawa a jihar baya domin ganin ya samu nasara.
Wadannan jam’iyyu da-dama, sun bayyana cewa Inuwa Yahaya, wanda ya tsaya a karkashin jam’iyyar APC, ya fi dukkan su cancanta da ya rike jihar.’Yan takarar su kace wannan ya sa su ka dauki matakin mara masa baya.
KU KARANTA: ‘Dan takara ya nemi a rusa takarar da Buhari da Atiku su kayi a 2019
Wadannan ‘yan siyasa da ke karkashin lemar wata kungiya mai suna Interparty Advisory Council watau IPAC, sun ce wanda jam’iyyar APC ta tsaida ya fi sauran ‘yan takara 30 da ake da su cancanta da rike jihar ta Gombe.
Wannan kungiya ta IPAC ta gamayyar jam’iyyun siyasar Najeriya tace ta ajiye duk wani banbancin ra’ayi ko alaka wajen tsaida ‘dan takarar, inda tayi ittifakin cewa Inuwa Yahaya ne zai kawowa Gombe cigaban da ake bukata.
Jam’iyyun siyasar da su ka hadu wajen cin ma matsaya game da zaben Gwamnan da za ayi a jihar ta Gombe sun hada da jam’iyyar Accord Party, DPP, ADC ACD, AD, MPN, CAP, BNPP, APA, AA, MMN, ANP, da kuma HDP.
Sauran jam’iyyun da ke tare da APC su ne, UPN, NCP, UPP, NCMP and PAC. Yanzu haka dai gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo yana shirin kammala wa’adin sa na biyu ne a karkashin PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng