Jam’iyyar APGA ta kori Victor Oye a matsayin shugaba, ta kuma sanar da madadinsa nan take

Jam’iyyar APGA ta kori Victor Oye a matsayin shugaba, ta kuma sanar da madadinsa nan take

  • Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta tsige shugabanta na kasa, Victor Oye
  • Har ila yau, jam'iyyar ta kuma sanar da dakatar da wasu mambobinta guda shida
  • Ta yi hakan ne bisa zarginsu da ayyukan adawa da jam'iyya, rashin da'a da kuma halin da zai iya kawowa jam'iyyar zubewar mutunci da sauransu

Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta sanar da korar wani shugaban bangaren jam’iyyar, Victor Oye.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 15 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Babu wasu ‘yan bindigan da suka yi sansani a Dajin Falgore na Kano - Ganduje

Jam’iyyar APGA ta kori Victor Oye a matsayin shugaba, ta kuma sanar da madadinsa nan take
Jam’iyyar APGA ta kori Victor Oye a matsayin shugaba, ta kuma sanar da madadinsa nan take Hoto: APGA National Headquarters Abuja
Asali: Facebook

Jam’iyyar ta nada Cif Jude Okeke a matsayin shugaban riko na kasa.

Mai magana da yawun APGA, Ikechukwu Chinyere, ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyar ta kuma sallami wasu mambobinta su shida.

Cinyere ya lissafa sunayensu a matsayin:

1 Chinedu Obidigwe,

2 Hamman Ghide,

3 Sylvester Ezeokenwa,

4 Adamu Musa,

6 Chief Okogbuo,

7 Ifeanyi Mbaeri.

Ya ce an dakatar da shuwagabannin na APGA daga jam'iyyar har sai baba ta gani saboda ayyukan adawa da jam'iyya, rashin da'a da kuma halin da zai iya kawowa jam'iyyar zubewar mutunci da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Ka fara tattara komatsanka yanzu, PDP ta aikawa gwamnan APC sakon barin kujerarsa

Ya kara da cewa NEC na jam’iyyar sun kuma yanke shawarar soke hana tsayawa takarar da aka yiwa mutum biyar da ke neman tsayawa takarar Gwamna a jihar Anambra.

Bangaren da Victor Oye ke jagoranta ne ya hana su takarar.

Wadanda aka hana takarar sun hada da Sullivan Nwankpo, Okafor Smart, Chukwuma Umeoji, Ozoka Ifeanyi, da Nnamdi Dike.

A jawabin amincewa da nadinsa, Jude Okeke wanda aka rantsar a wurin taron ya ce da alama a cikin shekaru da suka gabata; APGA ta kasance cikin kwanciyar hankali da kasancewar Anambra a matsayin Jiha daya tilo da take da ita amma arzikin jam'iyyar zai bunkasa a karkashin jagorancinsa, TVC News ta ruwaito.

A wani labari na daban, an zargi gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da yin watsi da yankin Edo ta Arewa ta hanyar rashin kafa wani aiki ko guda a yankin.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ne ya yi wannan zargi a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, yayin taron shugabannin jam’iyyar APC a mahaifarsa, a Iyamho, Edo ta Arewa.

An tattaro cewa tsohon gwamnan ya dawo da gwagwarmayar siyasar da wanda ya gaje shi kan rashin kaddamar da mambobin majalisar dokoki 14 da aka zaba a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng