Da duminsa: An rantsar Farfesa Mahmoud Yakubu matsayin shugaban hukumar INEC

Da duminsa: An rantsar Farfesa Mahmoud Yakubu matsayin shugaban hukumar INEC

- Farfesa Mahmoud Yakubu ya kafa tarihin da babu wanda ya taba kafawa a tarihi hukumar INEC

- Shine mutumin farko da zai yi tazarce kan kujerar tun lokacin da aka kafata

- Ya gaji Farfesa Attahiru Jega da ya kammala wa'adinsa a shekarar 2015

An rantsar da Farfesa Mahmood Yakubu karo na biyu a matsayin shugaban hukumar gudanar da zaben kasa watau INEC.

Shugaba Buhari ya rantsar da shi ne ranar Laraba a taron zaman majalisar zartaswa da ya gudana a fadar shugaban kasa, Aso Villa.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmaad, ya bayyana hakan a shafinsa na Tiwita.

"Mun nuna a zabukan baya-bayan nan cewa abubuwa na gyaruwa kuma zabuka zasu cigaba da gyaruwa," Farfesa Mahmoud ya bayyana.

"Wannan babban aiki ne. Wannan tarihi ne. Babu dan Najeriyan da ya taba zama shugaba INEC sai biyu. Wannan aiki ne kuma zan yi shi kamar yadda na rantse."

Da duminsa: An rantsar Farfesa Mahmoud Yakubu matsayin shugaban hukumar INEC
Da duminsa: An rantsar Farfesa Mahmoud Yakubu matsayin shugaban hukumar INEC Credit: Bayo Omoboriowo
Source: Twitter

KU DUBA: Shugaba Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisa, Munguno

Majalisar dattawa a ranar Talata 1 ga Disamba, ta tabbatar da nadin Farfesa Mahmood Yakubu, a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC na karin shekaru biyar.

Tabbatar da shi ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar dattawa kan INEC karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya, ta gabatar a zauren majalisa kuma aka bukaci a amince da shi.

Sanatocin sun siffanta Farfesa Yakubu a matsayin wanda ya cancanci cigaba da zama shugaban hukumar.

Mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Farfesa Maumoud Yakubu domin zama shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC karo na biyu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanto a zauren majalisa.

Shugaban kasan ya bukaci majalisar tayi gaggawar tabbatar da Farfesa Yakubu saboda ya kara shekaru 5 a INEC. Buhari ya bayyana hakan ne a wasikar da ya aike majalisar, kuma shugaban majalisar Ahmad Lawan ya karantawa Sanatacoi ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2020.

Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP a majalisar dattawa sun shirya domin hana a amince da sabon wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu a hukumar INEC.

KU DUBA: Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel