Kwadayi Ya Jawo Mana: Jagora a PDP Ya Fadi Wadanda Su ka Yi Sanadiyyar Fadi Zabe

Kwadayi Ya Jawo Mana: Jagora a PDP Ya Fadi Wadanda Su ka Yi Sanadiyyar Fadi Zabe

  • Bode George ya fito a mutum ya nunawa jam’iyyar PDP sanadiyyar rashin nasararta a zabukan da aka shirya a bana
  • A matsayinsa na Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, jigon ya na ganin shugabannin PDP na zamanin yau sun saki layi
  • Cif George ya zargi ‘Yan NWC da nuna kwadayi a fili a wajen tsaida ‘yan takara, ya na so yanzu a duba inda matsalolin su ke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Olabode George wanda ana yi masa kallon kusa a jam’iyyar PDP, ya zargi wasu ‘yan majalisar NWC da zama silar rashin nasararsu.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Punch ta ce Olabode George ya na ganin shugabannin PDP sun jawo mata cikas.

Kara karanta wannan

Wayyo Gida Na: Jigon PDP Ya Kai Kuka, Gwamnatin APC Za Ta Rusa Masa Muhalli

2023 PDP
Shugabannin Jam'iyyar PDP Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

PDP NWC ta biyewa son kudi a 2023?

A cewar ‘dan siyasar, wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP da ke rike NWC sun rika bada takara ga wadanda su ka fi kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin cefanar da tikitin takara da aka rika yi ne Bode George ya ce PDP ta sha kashi a hannun jam’iyyar APC a zabukan bana da aka yi.

Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasar ya ce a zaben jiharsa ta Legas, jam’iyya ta kaucewa tafarkin da iyayen gidansu su ka kafa ta a kai.

George yake cewa lokaci ya yi da za a komawa tsarin asali idan ana so a lashe zabe, tuni dai ya ajiye duk adawar da yake yi wa Bola Tinubu.

Jawabin Bode George a kan halin PDP

"Fitaccen misali shi ne a zaben fitar da gwanin gwamnan Legas; sai su turo mutanen da ba su zama a nan, wadanda ba su da alaka da nan domin shirya zaben tsaida gwani.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa za su yi binciken yadda ake saida Digiri kamar ruwan leda a Jami’a

Ta ya wani daga waje zai fi ka sanin inda yake yoyo a cikin dakinka. A lokacin da su ka zo, maimakon su bari ayi zabe, sai su ke neman ‘yan takara, su ka zama injin ATM.
Su na gamawa, sai su koma wajen sashen gudanarwa na kasa domin tabbatar da wanda su ka marawa baya. Ba zan yi wani karin bayanin abin da ya wuce wannan ba.

- Bode George

Mecece mafita ga shugabannin PDP?

Daily Post ta ce jigon ya yi kira da aka kafa kwamitoci sulhu domin dinke baraka a gidan PDP.

George ya nuna akwai bukatar a zauna ayi karatun ta-natsu domin ganin abubuwan da su ka faru a zaben 2023 saboda a dauki darasi domin gaba.

Fadan Matawalle v Dauda Lawal

A rikicin siyasar Zamfara, ana da labari Bello Muhammad Matawalle ya kira Dauda Lawal makaryaci da mayaudari a sabon martanin da ya yi.

Kara karanta wannan

A shirya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi mamayar da Tinubu zai yi wa 'yan boye dala

Matawalle yake cewa ya hana Dauda Lawal lakume N300m, kuma an ba shi kwagilar tireloli 120 na taki amma tireloli 10 rak ya kawo jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng